Gwamnatin Jihar Neja Ta Yi Ta’aziyyar Marigayi Muazu Wali

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A ranar Asabar ne gwamnatin jihar Neja ta nuna kaduwarta da alhininta akan rasuwar Walin Kontagora, Alhaji Muazu Wali.

Rahoto ya nuna cewa, Marigayi Wali ya rasu ne a ranar 5 ga watan Maris a Asibitin gwmanatin tarayya da ke garin Bida bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Ahmed Matane, ya bayya haka a tataunawarsa da manema labarai ranar Asabar, ya ce, gwamnatin jihar da al’ummar jihar za su yi kewar marigayi Walin Kontagora.

“Marigayi Wali mutum ne tsayyaye wanda ya bayar da gudumwarsa waje bunkasa ihar Neja.

“Za mu cigaba da tunawa dashi akan yadda ya ke aiki tukuru da gaskiya ba tare da nuna banbanci ba,” inji shi.

Sakataren gwamnatin ya kuma mika ta’aziyyar gwamnatn jihar ga iyalan marigayin da kuma al’umma masarautar Kontagora gaba daya.

“Muna addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma sanya aljjana fiddausi ta zama makomarsa.

An dai haifi Marigayi Wali, a ranar 15 ga watan Disamba 1940.

Ya rasu ya bar mace daya mai suna Hajiya Hauwa Wali, wadda babbar sakatariya ce a fadar gwamnatin jihar Neja da kuma yara da dama.

Share.

About Author

Leave A Reply