Gwamnatin Kano Za Ta Horas Da Likitoci Sabbin Hanyoyin Jinyar Cutar Kansa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, ya ce, jihar za ta maqufa wajen haxa kai da masana don horas da ma’aikatan jinya da likitoci da zarar ta kammala cibiyar kula da cutar kansa ta zamani.

Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da ya karvi baquncin qungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta qasa a majalisar jihar Kano.

Hakan na qunshe ne a cikin wata sanarwa da Abba Anwar, Babban sakataren labarai na gwamnan ya fitar a ranar Alhamis a Kano.

Gwamnan ya ce, “nan ba da daxewa ba, za mu haxa hannu da wasu qwararru a fannin kula da cutar kansa, don su zo su horar da ma’aikatan jinyarmu da likitocinmu kan maganin cutar kansa. Wannan gwamnatin ta ba da muhimmanci sosai ga vangaren kiwon lafiya na jihar, kuma babu shakka mun inganta fannin kiwon lafiya kuma ina farin ciki da wannan muhimmiyar qungiyar ta gane hakan.”

“Cibiyarmu ta cutar kansa tana da kimar qasa da qasa. Na kasance a Melbourne, Ostiraliya, lokacin da na ziyarci cibiyar kula da ciwon sanqararsu kuma na yi alqawarin sanya wani abu makamancin haka a Kano. Wannan shi ne abin da muke qoqarin aiwatarwa a yanzu,” in ji Ganduje.

A cewarsa, saboda yawaitar tasirin da al’ummar jihar ke yi wa cibiyoyin kiwon lafiya ya sa gwamnatina ta yanke shawarar kafa qarin asibitoci.

“kasancewar kano xaya daga jihohin da suka fi yawan jama’a a qasar, hakan na nufin ana buqatar qarin wuraren kiwon lafiya. A wasu lokuta muna karvar marasa lafiya daga Jamhuriyar Nijar mai nisa, ban da waxanda ke zuwa daga wasu jihohin tarayyar,” in ji shi.

Gwamnan ya yaba wa mambobin qungiyar kan yadda suke yin aikinsu yadda ya kamata.

Shugaban qungiyar, Kwamared Ibrahim Maikarfi, ya yaba wa gwamnan kan nasarorin da ya samu a vangaren kiwon lafiya a jihar.

“Yana iya ba ka sha’awa ka sani cewa tunda ka hau mulki a matsayinka na Gwamna, mambobinmu ba su tsunduma cikin wani yajin aiki ba. Wannan ya nuna irin namijin qoqarin da kuke yi da vangaren,” in ji Maikari.

 

Share.

About Author

Leave A Reply