A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Kebbi ta fara raba filaye 22,000 ga al’umma jihar marasa karfi don su gina muhalli.
Alhaji Abubakar Sadiq, kwamishinan filaye da gidaje ya bayyana haka a taron manema labarai da aka yi gidan gwamnatin jihar Kebbi.
Ya ce, Gwamnan jihar Abubakar Atiku-Bagudu ya samar da shirin don al’ummar jihar su samu muhall na.
Kwamishinan ya kuma ce, an samar da shirin don a rage mastalar muhalli da ake fama da su a jihar.
Ya kuma ce, a cikin garin Birnin Kebbi, babban birinin jihar ake da fuloti fiye 7,000 da za a raba ga al’umma.
Ya ce, sauran fulotu 1,500 za a samar da su ne garuruwan Argungu, Yauri and Zuru, ya yi da kuma fulotu 535 za a raba a sauran kananan hukumomin jihar.
Ya kuma shawarci al’umma jihar masu sha’awar mallakar filayen su gaggauta karba tare da cike fom daga ma’aikatarsa ko kuma ofishohinmu da ke sassan jihar.