Gwamnatin Legas Ta Tallafa Wa Manoma 6,650 Da Kayan Aiki

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnatin jihar Legas ta samu nasarar tallafa wa manoma 6,650 da kayan aiki da kuma kudade don tabbatar da bunkasar abinci a fadin jihar.

Shugaban hukumar bukasa harkar noma na jihar (LASADA), Dr Olamilekan Pereira-Sheteolu ya bayyana haka a yayin ziyararsa filayen gonan manoman da suka amfana da tallafin a garin Ikorodu ranar Lahadi.

Pereira-Sheteolu ya kara jaddada bukatar tabbatar da samar da abinci ga al’umma jihar.

Ya ce, dole a karfafa manoman jihar don ciyar da al’umma jihar da ke karuwa a ‘yan shekarun nan kuma bukatar abinci na kara karuwa.

Ya ce, shirin na son kara jaddada wa manoma cewa, harkar su na noma babbar sana’a ce, ya kuma kamata su rike shi da hannu biyu biyu don karuwarsu da kuma sauran al’umma.

Mai magana da yawun manoman da suka amfana ya nuna godiyarsa ga gwamnati akan tallafin ya kuma yi alkawarin amfani da tallafin yadda ya kamata.

 

Share.

About Author

Leave A Reply