Gwamnatin Neja Ta Kaddamar Da Sayar Da Takin Zamani

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnatin jihar Neja ta fara sayar da takin zamani don gudanar da harkar noman bana a kan kudi N8,000 kowanne buhu.

Gwamna Abubakar Bello na jihar wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Ahmed Ketso a taron, ya ce, jihar ta kaddamar da sayar da takin ne da tan 15,000 inda za a raba a kananan hukumomi 25 na jihar.

“Zuwa yanzu an kawo motoci 27 na takin an kuma riga an raba su ga kananan hukumomin jihar 25 don a sayar wa manoma, don su fuskanci harkar noman wannan shekarar na 2021,” inji shi.

”Mun yi haka ne don karfafawa manoma samun damar fuskantar harkar noma a kan lokaci ba tare da bata lokaci ba, wanda haka kuma zai taimaka wajen bukasa samuwar abinci a fadin jihar dama kasa baki daya.

A jawabinsa, shugaban kungiyar manoman jihar, Alhaji Shehu Galadima, ya bukaci gwamnati ta kara samarwa manoma tallafi kan kayan aikin noma kamar su trakta don ta haka ne za a iya tabbatar da dorewar noma a jihar.

 

Share.

About Author

Leave A Reply