Gwamnatin Tarayya Da Likitoci Sun Sa Hannu A Yarjejeniyar Dakatar Da Yajiin Aiki

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnatin tarayya da kungiyar likitocin Nijetiya sun sanya hannu akan yarjejeniyar fahintar juna da zai kai ga dakatar da yajin akin da kungiyar ke yi a halin yanzu.

Wannan yarjejeniyar shi ne na biyu a cikin ‘yan kwanakin nan, don kuwa an sanya hannu a kan yarjejeniyar farkon a ranar 31 ga watan Maris, amma kungiyar likitocin suka yi watsi da yarjejeniyar.

Ministan kwadago Santaa Chris Ngige, ya bayyana haka ranar Asabar a Abuja, bayan da aka shiga wata tattaunawa tsakanin gwamnatin da wakilan kungiyar lilitocin.

Ngige ya kuma ce, taron na ranar Asabar na da matukar mahimmanci saboda a nan ne aka sake yi wa yarjejeniyar kwaskwarima aka kuma sanya hannu don kowa ya amince da abin da aka cimma.

Ya ce, an samu matsaloli ne a wajen biyan albashin manyan likitocin, yayin da wasu suka samu albashi har sau biyu wasu kuma daga cikin su basu samu ko kwabo ba

“A kan haka ne muka kafa kwamitin mutum biya don tattauna tare da fito da yadda za a fuskanci lamarin, an kuma basu kwanaki uku na su gama bincike tare da kawo rahoton su don a aiwatar.

“Daga na ne za kuma a mika sunayen da suka fito dasu bangaren kula da albashi na IPPIS na ma’aikatar lafiya don a biya kudaden su ba tare da wani bata lokaci ba,’’ inji Ngige.

Shugaban kungiyar likitocin, Dr Okhuaihesuyi Uyilawa, ya yi alkawarin mika yarjejeniyar da aka cimma ga taron kwamitin jihohi na kungiyar don su bayar da shawarar yadda za a fuskanci lamarin, a ranar 1 g watan Afrilu ne dai kungiyar ta shiga yajin aikin inda take neman a biya mata bukatun ta.

Share.

About Author

Leave A Reply