Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Matan Karkara 2,510 A Jihar Abiya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Ma’aikatar harkokin jinkai ta bayana cewa, ta samu nasarar tallafa wa matan karkara 2, 510 da N20,000 kowanne su a matsayin tallafi na musamman a jihar Abia.

Wadanda suka amfana sun fito ne daga dukkan kanana hukumomin iihar gaba daya.

Ministar ma’aikatar, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayana haka a sanarwa da jami’ar watsa labarai na ma’aikatar,  Mrs Rhoda Iliya ta raba wa manema labarai a garin Abuja ranar Asabar.

Sanarwa ta kuma ce, mata masu fama da nakasa ma sun amfana da tallafin.

Minstar wadda babban sakataren ma’aikatan Alhaji Bashir Alkali ya wakilta ya ce, za kuma a raba irin wadanna kudade ga mata masu karamin karfi a fadin tarayyar kasar na gaba daya har ma da yankin babbar birnin yarayya Abuja.

“Muna fatan raba wa mata 2,510 a dukan kanana hukumomin jihar gaba daya. Ana sa ran kudaden za su taimaka wa matan wajen bunkasa harkokin kasuwancin su.

Sanarwa ta kuma yaba wa mataimakin gwamnan jihar Mr Ude Okochukwu, akan gudumwarsau wajen ganin nasara aikin raba kudaden..

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply