Gwamnatin Zamfara Ta Karyata Batun Ba ‘Yan Bindiga Tallafi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnatin Zamfara ta musanta wani rahoto da kafafen yada labarai na yanar gizo suka bayar cewa ta ba da manyan motocin kirar Hilux ga tubabbun ’yana Bindga a jihar.

 

A lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a ofishinsa a ranar Talata, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Alhaji Abubakar Dauran, ya bayyana rahoton a matsayin “Mara tushe ”.

 

“Wannan hakika babu gaskiya a ciki, kage ne na marubuci da kuma wata magana mara tushe wanda aka shirya domin shafa wa kokarin Gwamna Bello Matawalle da kuma kokarin da gwamnatinsa ke yi na magance matsalolin tsaro a jihar.

 

“Kun san zai zama wawanci ga duk wani mai tunani mai kyau idan aka ce gwamnatin da ta tsaya tare da bayar da gudummawar motocin Hilux 200 don saukake ayyukan jami’an tsaro a jihar za ta kuma ba motocin motoci ga ‘yan Bindga ta kowane irin tsari.”  Inji shi

 

A ranar Talata ne wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta fitar da wani rahoto da ke zargin cewa gwamnatin Zamfara ta ba da motoci uku ga ‘yan ta’addan da suka tuba wadanda a yanzu suke amfani da su wajen aikata laifi, ta yadda suka ci amanar yarjejeniyar zaman lafiya da suka kulla da gwamnatin.

 

Zargin ya zo ne a kan wani harin da aka kai da safiyar Litinin a kan garin Janbako da ke karamar Hukumar Maradun inda aka kashe kimanin mutane 10.

 

Share.

About Author

Leave A Reply