Hatsairn Jirgin Sojoji: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Ta’aziyya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayuwarsu a hatsarin jirgin sama da ya auku a yankin Abuja jiya Lahadi

Shugaban majalisar ya nuna kaduwarsa akan hatsarin wanda ya yi sanadiyar mutuwar dukkan mutanen da ke cikin jirgin.

Shugaban majalisar ya bayyana haka ne a sanarwa da ya raba wa manema labarai ta hanun jami’in watsa labaransa, Mr Ola Awoniyi a Abuja.

Ya mika ta’aziyya tare da addu’ar Allah ya gafarta masu ya kuma bayar da hakurin jure rashin.

Ya kuma yi wa rundunar sojin sama ta’aziyya ya kuma bukaci a kara daukar matakan kariya don kare aukuwar irin wannan hatsarin anan gaba.

Haka kuma shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da sojin sama, Hon. Shehu Koko (APC-Kebbi), ya mika ta’aziyya ga shugaban kasa akan hatsarin da jirigin saman ya yi, ya kuma nuna damuwa akan hatsarin ya yi adduar Allah ya gafarta wa wadanda suka mutu a hatsarin, ya kuma bukaci a binciki cikakken dalilin aukuwar hatsarin da nufin dakile aukuwar irin haka ana gaba..

 

Share.

About Author

Leave A Reply