Daga Idris Khalid
A yau Asabar 23 ga watan Mayu ne Shaikh Dahiru Usman Bauchi, ya gudanar da Sallar Idi karama a gidansa da ke Bauchi.
Alhaji Ibrahim Shaikh Dahiru Bauchi shine ya jagoranci Sallar Idin, a yayin da Shehin Malamin ya kasance daga cikin wadanda suka shaidi sallar Idin na bana.
Dandazon jama’a ne suka halarci wannan Sallar Idin. An fara Sallar Idin ne da karfe 9 na safiya inda aka kammala zuwa 9:40 na safiyar yau.
Ga hotuna da suke akwai wadda Idris Khalid ya dauko mana.
Ku ci gaba da kasancewa da mu don sauraron yadda ta kaya.