Hukumar FRSC Za Ta Fara Fatattakar Masu Sayar Da Barasa A Tashar Mota

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar kiyaye hadurra FRSC ta bayyana shirinta na fara fatattakar masu sayar da barasa a tashoshin motoci a kasar nan don rage yadda direbobi ke yawan shan giya a yayin da suke tuki.

Mr Olusegun Aladenika, shugaban hukumar a yankin Ore, ta jihar Ondo ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai ranar Laraba, ya ce, daukar wannan matakin zai taimaka wajen rage asarar rayuka da dukiyoyin al’umma a kan titunan kasar nan.

Ya kuma nemi hadin kan shugabannin kungiyar direbobi ta NURTW a yakin da suka daura da shan giya a tashoshin motar kasar nan..

Daga nan ya kuma ce, a lokutta da dama hukumar FRSC ta gudaar da gangamin fadakar da al’umma akan sharrin da ke tattare da shangiya yayin tuki ga direbobinmu.

Ya kuma kara da cewa, dole direbobi su bi dukkan dokokin tuki tare da kare rayuwar al’umma wanda kuma shi ne babbar burin hukumar.

Share.

About Author

Leave A Reply