Hukumar NSCDC Ta Qara Wa Jami’anta 25 Girma A Jihar Yobe

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

 

 

 

 

 

 

 

Hukumar samar da tsaro ta NSCDC  reshen jihar Yobe ta yi qarin girma ga jamiánta 25 a jihar.

Da ya ke jawabi a wurin taron, shugaban hukumar a jihar, Mista Ayinla Olowo ya yi kira ga jamián da su dage da qoqari don ganimn sun sauke nauyin da ke kansu na sabon matsayin da su ka samu.

Shugaban ya ce qarin matsayin zai taimaka masu wurin ci gaba da bunqasa qwarewar aikin su, ya kuma roqi Alla da ya taimaka masu don ganin sun yi aikin kamar yadd aya kamata domin cigaban rundunar da kuma qasa bakixaya.

Mista Ladan Amadu na xai daga cikin waxanda su ka samu qarin girman, ya bayyana farin cikinsa tare da alqawirin dagewa don ci gaba da aiki kamar yadda dokar qasa ta tanadar.

 

Share.

About Author

Leave A Reply