Ibrahimovic Zai Buga Wasan Hamayyar Birnin Milan

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Ana sa ran fitaccen dan kwallon kafa Zlatan Ibrahimovic zai fafata a wasan hamayya na Serie A da AC Milan za ta kara da Inter Milan, a cewar kocinsa Stefano Pioli.

Dan wasan mai shekara 38, wanda ya koma AC Milan a karo na biyu a watan Janairu, bai buga gwabzawar da aka yi tsakanin Milan da Hellas Verona ba, wadda suka tashi ci 1-1 ranar Asabar din makon jiya saboda rashin lafiyar da ke damunsa.

Sai dai da alama ya murmure kuma zai iya fafatawa a wasan na hamayya wanda za a yi a Derby della Madonnina ranar Lahadi.

Ranar Asabar Pioli ya ce: “Yau yana can yana atisaye tare da takwarorinsa kuma idan ya murmure sosai za mu sanya shi a wasa.”

Ko da yake Milan na matsayi na tara a gasar Serie A, inda take da maki 19 a kasan mai matsayi na biyu, Inter, ba a taba zura masu kwallo ba tun lokacin da Ibrahimovic ya koma kungiyar a watan jiya.

Pioli ya yi amannar cewa tsohon dan wasan na Sweden shi ne zai cire musu kitse a wuta a fafatawar da za su yi da tsohuwar kungiyarsa, wadda ba ta sha kashi a gasar lig ba tun dokewar da Juventus ta yi mata a watan Oktoba.

“Za mu fuskanci kungiyar da ba ta sha kashi a wasa ba tsawon lokaci,” in ji Pioli.

A cewarsa: “[Ranar Lahadi] dole mu sanya Ibrahimovic a wasan domin ya zaburar da mu. Dole mu yi amfani da damarmu.”

Share.

About Author

Leave A Reply