Ibtila’in Gobara: Sanata Barkiya Ya Bada Gudummawar Naira Miliyan 20 Ga ‘Yan Kasuwar Katsina

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Zahraddeen Sirajo Abbas

A jiya ne Sanata Abdullahi Kabir Barkiya ya kai ziyarar jaje ga ‘yan kasuwar da ibtila’in gobara ya afkawa a Babbar Kasuwar Jihar Katsina.

A yayin ziyarar jajen Sanata Barkiya ya nuna damuwa kasantuwar lokacin da lamarin ya faru ya yi tafiya zuwa Kudu wajen wani aiki.

Ya ce; “naso a ce ni ne mutum na farko da ya fara ziyartarku, amma Allah bai so ba saboda halin tafiya, saboda haka ina nuna alhini da jaje gareku akan wannan jarabawa.” Inji shi.

Haka nan kuma a yayin ziyarar, Sanata Barkiya ya ba ‘yan kasuwar gudummawar kudi Naira Miliyan 20. “A bisa wannan kuma nake cewa a yi hakuri da abin da ya samu. Na baku gudummuwar Naira Miliyan 20. Allah Ya mai da mafi alkhairin abunda aka rasa, Allah Ya kare afkuwar jarabawa irin wannan nan gaba.”

A lokacin da yake gabatar da jawabin godiya, shugaban ‘yan Kasuwar, Alhaji Labaran Albaba ya nuna murna da jin dadi dangane da wannan ziyarar jaje da Gudunmuwar. har ma ya ce wadanda suka zo kafin Sanatan ba su fi shi da komai ba  “muna godiya a madadin ‘yan Kasuwa. Allah Ya kara mana irinku a Jahar Katsina.”

Daga Zahraddeen Sirajo Abbas

Share.

About Author

Leave A Reply