INEC Ta Fara Gangamin Faxakar Da Al’umma A Kan Rajistar Katin Zabe A Jihar Filato

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar zave mai zaman kanta ta qasa (INEC), a ranar Alhamis, ta shirya wata hanya don wayar da kan mazauna Filato kan ci gaba da rajistar masu zave (CVR).

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, jami’an INEC sun bi jerin gwano a manyan tituna a cikin garin Jos da Bukuru, suna yin jawabi ga mazauna tare da rarraba takardu game da aikin na CVR.

Sylvanus Yepe, Shugaban sashin ilimin INEC, da wayar da kan masu zave, ya ce, maqasudin wannan baje kolin shi ne don a sanar wa mutanen Filato cewa CVR ta fara aiki.

Yepe ya bayyana cewa, wannan atisayen na ‘yan Nijeriya ne da suka kai shekaru 18 zuwa sama, da kuma waxanda har yanzu basu yi rijistar ba.

A cewarsa, an fara atisayen ne a ranar 28 ga watan Yunin kuma zai xauki tsawon shekara guda.

Yepe ya qara da cewa, waxanda suka cancanci kaxa kuri’a za su fara buqatar yin rajistar ta intanet sannan su kammala aikin rajistar a ofishin INEC xin da kansu.

Ya ci gaba da cewa, “masu niyyar yin rijista na iya amfani da manjahar rajistar INEC ta yanar gizo (cvr.inecnigeria.org) don yin rajistar kafin su ci gaba zuwa kowane ofishin INEC don kammala rajistar. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, a ranar 26 ga watan Yuli, waxanda suka kammala rajistar su ta yanar gizo za a xauke su hoto.”

“Ana sa ran za su je ofisoshin qananan hukumomi ko hedikwatar jihar ta INEC a Jos don xaukar hoton fuskarsu da yatsun hannunsu,” in ji shi.

Ya yi kira ga duk waxanda suka cancanci zama a Filato su fito qwansu da qwarqwata kuma a kan lokaci su yi rajista.

Yepe ya kuma shawarci waxanda ke da katunan zave na dindindin (PVCs) da su nemi hanyar yanar gizo domin sauya su.

Ya kuma buqaci waxanda ke da niyyar sauya rajistar su ko gyara bayanan su da su yi hakan ta hanyar yanar gizo.

Ya qara da cewa, za a yi rajistar ne ta hanyar bin qa’idojin kariya na cutar Korona.

Share.

About Author

Leave A Reply