Iran Za Ta Maida Martani Kan Harin Da Aka Kaiwa Jirgin Ruwanta

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Umar Shu’aibu

Iran ta tabbatar da kudirinta na maida martani bisa harin da aka kai wa Jirgin Ruwanta a Tekun Maliya a farkon makon nan da muke ciki.

Kakakin rundunar tsaron kasar Iran Manjo Janar Abu Al-Fadel Shekarji ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da kafar watsa labarai na Sputnik.

“Muna bukatar mu tabbatar da asalin abin da ya faru. Idan muka gano tushen harin da aka kaiwa jirgin, tabbas za mu maida martani, ba za mu taba yin shiru ba. Ko ta halin yaya dai, an yi niyyar kai wa jirgin hari ne, kuma a yanzu abubuwa daban-daban na iya faruwa ga jirgi. Amma ba za mu iya yanke hukunci kan abin da za mu yi ba sai bayan mun kammala bincikenmu.” Cewar Kakakin.

Ya kuma ƙara da cewa, Iran na zargin abokan gaban ta na asali, Amurka da Isra’ila da kuma manyan ƙawayensu a Gabas ta Tsakiya da hannu a cikin wannan harin.

Share.

About Author

Leave A Reply