Isra’ila Ta Kai Wa Jirgin Ruwan Iran Hari

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Umar Shuaibu

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim dake ƙasar Iran ya wallafa cewa wata majiya da ba a bayyana sunanta ba ta bayyanawa Jaridar ‘New York Times’ na kasar Amurka cewa Kasar Isra’ila ta aikewa kasar Amurka sakon cewa ta kaddamar da hari a kan Jirgin ruwan ƙasar Iran a Tekun Maliya.

Jaridar ‘New York Times’ ta ruwaito cewa Kasar Isra’ila ta kaddamar da harin ramuwar gayya ne na wani harin da suka ce Ƙasar Iran ta kaddamar akan Jirgin ruwan ƙasar ta Isra’ila.

A jiya Talata da daddare ne dai wasu majiyoyi suka ruwaito wani hatsari da ya rutsa da Jirgin ruwan Saviz mallakar Iran a Tekun Maliya.

Tasnim ta ruwaito cewa hatsarin ya faru ne sakamakon fashewar wasu Nakiyoyi a cikin Jirgin Ruwan.

An ajiye Jirgin na Iran Saviz ne a Tekun Maliya shekarun da suka gabata domin taimakawa Jiragen Ruwan Kasuwanci.

Kakakin Fadar Pentagon yayi da’awar cewa ba shi da wani bayani dangane da hatsarin Jirgin Ruwan Iran Saviz a Tekun Maliya.
Ya kuma musanta duk wani rawar da sojojin Amurka za su taka a tarwatsewar Jirgin Ruwan Iran Saviz da ke cikin Tekun Maliya, yana mai jaddada cewa babu wani sojan Amurka da ke da hannu a harin.

Sai dai har zuwa haɗa wannan rahoton, hukumomin Iran ba su faɗi komai ba dangane da hatsarin Jirgin Ruwan.

Share.

About Author

Leave A Reply