Jihar Bauchi Ta Samar Da Ma’aikata 2,261 Don Yi Wa Al’umma Rigakafin Zazzabin ‘Yellow Fever’

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Bauchi ta bayyana cewa, a halin yanzu ta samar da ma’aikata 2,261 an kuma watsa su dukkan bangarorin jihar don fuskantar yi wa al’umma jihar allurar rigakafin zazzabin ‘Yellow Fever’.

Mr Bakoji Ahmed, shugaban shirin a jihar ya bayyana haka a a tattaunawarsa da manema labarai a garin Bauchi ranar Juma’a.

Ya kuma kara da cewa, kowanne tawaga zai kasance da mutum 10 ciki har da jagororinsu.

Ya kuma ce, hukumar za ta aika da magungunan dukkan kananan hukumomin jihar guda 20 za kuma ayi amfani da cibiyoyin bayar da kulawa na musamman guda 10 a fadin kananan hukumomin jihar guda 20.

“Hukumar Kula da Lafiyar nada tawaga 1,968 yayin tawagar jiihar zai kunshi 293 da su za a yi amfani wajen gudanar da rigakafin a fadin jihar gaba daya.

“Rigakafin sau daya ake yi, saboda haka duk wanda ya yi kwanan nan kada ya sake yi,” inji shi.

A nasa gudunmawar, Mr Seyi Nubi, jami’I daga UNICEF na yankin Bauchi ya ce, dukkan wma’aikatan za su tabbatar da suna amfani kayan kariya daga cutar korona don kada yada cutar ko kuma su kamau da ita.

Ya kuma bayyana cewa, za a tabbatar da an gudanar da rigakafin a iyakokin jiyar da sauran wurare masu muhimmanci.

Haka kuma, Dr. Rilwanu Mohammed, ya bayyana cewa, a shekarar 2020, mutun 30 suka kamu da zazzabin a karamar hukumar Ganjuwa, bayani ya kuma nuna cewa, mutum 10 ne suka mutu a cikinsu sakamakon kamuwa da cutar.

Ya kuma ce, kashi 50 na yara a karamar Alkaleri da Ganjuwa har yanzu ba a yi musu allurar rigakafin cutar ba, za a fara aikin rigakafin ne daga ranar 18 ga watan Janairu zuwa ranar 27 na 2021.

Share.

About Author

Leave A Reply