Jihar Kano Ta Fito Da Tsarin Jiyar Masu Cutar Korona A Gidajensu

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kwamitin kula da yaduwar cutar korona ta jihar Kano ta samar da tsarin da za a rika jiyar masu fama da cutar korona daga gidajensu a mastayin hanyar dakile yaduwar cutar a fadin jihar.

A ranar Asabar ne hukumar ta bayar da wanna sanarwa a takarar da jami’im watsa labaranta Mr Maikudi Marafa, ya sanya wa hannun.

Ya kuma kara da cewa, kwamishinna lafiya na jihar, Dr. Aminu Tsanyawa, ya kaddamar da shirin ya kuma ce ya zama dole a yi gangamin dakile yaduwa da bullowar cutar na korona a karo na biyu a fadin jihar.

Kwamishin ya ce, an horas da jami’an kiwon lafiya a jihar hanyoyin da za su gudanar da ayyukansu tare da samar musu da mashina don su samu shiga yankuna karkara don bayar da agajin gaggawa ga masu fanma da cutar.

“Dr Tsanyawa ya kuma hori ma’aikatan lkafiya da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu,” ini sanarwa.

Share.

About Author

Leave A Reply