Jihar Kwara Ta Ware Dala Miliyan 60 Don Gyara Hanyoyi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya kaddamar da shirin gyara hanyoyin jihar wanda ake sa ran za ta lakume Dala Milan 60.

A ranar Laraba ne Gwamnan ya kaddamar da shirin, kuma mataimakinsa Kayode Alabi, ya wakilce shi a bukin kaddamar da aikin gyara hanyoyin ya kuma ce, tuni gwamnatinsa ta bayar da Naira Miliyan 400 nata bangaren na hadakar kwangilar.

Ya kuma kara da cewa, gwamnati ba za ta iya tabbatar da tsaro da kuma shirin samar da abinci a gadin jihar ba n har babu ingantattun hanyoyin a fadin jihar, akan haka ta shiga yarjejeniya da wasu kungiyoyin kasashe waje don samar da ingantattun hanyoyin a jihar.

Gwamnatin mu ta bayar da Naira Miliyan 4000 a na ta bangaren na hadakar, ya kuma mika godiyar gwamnati ga Bankin Duniya da sauran kungiyoyin kasshe duniya masu bayar da tallafi a bisa hadin da goyn baya.

Al’ummar jihar sun nuna jidadinsu akan aikin samar da hanyar, suna mai cewa, lallai aikin zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci da na walwalarsu.

 

Share.

About Author

Leave A Reply