Jirgin Saman Sojin Saman Nijeriya Ya Yi Hatsari A Abuja

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Jirgin saman rundunar sojin Nijeriya mai lamba NAF201, dauke da mutum 6 tare da direbobinta da kuma ma’aikatan jigin ya fado a garin Abuja ana kuma da tabbacin dukkan mutanen da ke cikn jirgin sun mutu.

Jirgin samfurin B350, ya tashi ne daga Abuja da safiyar yau Lahadi kafin ya rikito ya kuma kashe dukkan mutane da ke ciki.

Bayanin tabbatar da hadarin ya fito ne daga shafin tiwita na ministan harkokin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya kuma kara da cewa, jirgin ya tashi ne da misalin karfe 10.39 na safe ya kuma fado ne a lokacin da yake kokarin sauka a tashar saukar jiragen sama na Abuja bayan da injin din jirgin ya samu mastala.

“Jami’an kashe gobara sun isa wiurn don kai dauki a halin yanzu, ” inji shi.

 

Share.

About Author

Leave A Reply