Jita-jitar Sayen Ramos: Asirin Real Madrid Zai Tonu!

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rahotanni daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid sun yi nuni da cewa, Sergio Ramos ya tubure akan barin kungiyar da ke taka leda a wasan La Liga na kasar Sipaniya.

Kafar AS Sport ta ruwaito cewa, Real Madrid na son ta karawa Ramos wa’adin shekara daya a kungiyar ba tare da karin albashi ba, shi kuma ya cije a kan sai dai a kara mishi shekara biyu tare da karin albashi.

Tuni dai Kungiyar ta Real Madrid ta fara farautar dan kwallon baya na Bayern Munich, wato Alaba, domin kaucewa ba-zata daga Ramos.

Ita kuwa Kungiyar Paris Saint Germain ta wasa wukarta ta baza koma wurin neman sayen Ramos. Tuni dai kungiyar da ke taka leda a Kasar Faransa ta sanar da cewa, za ta ninka wa Ramos albashinsa tare da wasu alawus na musamman matukar ya aminta zai koma wurinsu.

Masana harkar taka leda dai sun yi fashin baki da cewa, barin Ramos na iya tona asirin kungiyar kwallo ta Real Madrid, musamman bisa la’akari da cewa shi ne ginshikinta a wannan lokacin da ba su da zakakuran ‘yan wasa.

Share.

About Author

Leave A Reply