Kamata Ya Yi Farfesa Soyinka Ya Gode Wa Allah Da Buhari Wurin Gina Nijeriya, Inji Dr. Bature Abdul’azeez

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +
Wannan wata tattaunawa ce da Shugaban Kungiyar Hadaddiyar ‘Yan Kasuwa ta Nijeriya, Dr. BATURE ABDUL’AZEEZ inda ya yi bayanai masu zurfi kan maganganun da Farfesa Wole Soyinka ke yi kan gwamnatin Buhari. Ga yadda hirar ta kasance kamar yadda MUHAMMAD ABUBAKAR ya rubuto.
 
Me za ka ce game da wasu maganganu da Wole Soyinka ke ta faman yi a ‘yan kwanakin nan? 
 
Ai duk lokacin da ka ji Farfesa Soyinka yana magana toh ka dauka tamkar haushi ne na karen Turawa. kuma su Turawan nan wadanda suke kullum su so suke yi su kunna wutar wargaza Nijeriya. Mu mun yi yawan duniya, amma kasa mai arziki da yawa zai yi wahala a samu irin Nijeriya. Amma wadansu wadanda su kullum so suke yi su sayar da Nijeriya a idon turawa don a basu lambar yabo ta Nobel. Da turawa sun san halin Soyinka da ba su ba shi lambar yabo ta Nobel ba.
Ko me ya sa ka ce haka?
Saboda idan ka duba da kyau za ka ga cewa Soyinka bai taba yin wani abu walau na bayar da shawara ko taimakawa ci gaban kasa ba. Shi dai a takaice yana da tsohuwar gaba da Arewa da mutanen arewa da addinin arewa. Wannan ya rage a fahimci shin dattijo ne shi ko dattijon biri. Duk lokacin da ya yi magana da shi da NGOs miyagun cikinsu, wadanda aka basu aikin jefa Nijeriya cikin rudani, ba su da aikin fito da alherin Nijeriya. Kar ka dada kar ka rage ‘yan Nijeriya. Wai fa akan an ba shugaban kasa Buhari lambar yabo ta cewa shi ne sarkin yaki da Korona a Afirka, wannan ne fa kawai, sai ya zam bakin cikin Obasanjo, Soyinka da turawa ya motsa. Wai don a bakanta ran Nijeriya, sai aka ce Nijeriya ta sha gaban Indiya wurin mutuwar kananan yara. don Allah ka ji wannan magana.
To ya zancen ya ke?
Mun san Indiya cikinta da wajenta gwargwadon iko na zaga cikinta, Indiya da suke da mutum sama da mutum biliyan da doriya, akalla sun ninka Nijeriya sau da yawa. Kuma wadannan duk da na lissafa gabakidayansu, duk kauyen da ka sani a Nijeriya sun fi kauyawan Indiya wayewa. Amma ka ji don kin Allah wai mu muka fi su yawan mutuwar Jarirai. Toh kididdigar karya ce, kididdigar yarfe ce. Kididdigar kaskantar da Nijeriya ne. Yau din nan, aka ce, mutum 88,000 a rana daya sun kamu da Korona a Indiya. Mun san Shugabanninmu sun yi kokari, amma fa mun dafa musu da addu’a.
Iyayen gidan Farfesa a yadda suka so, bala’in da ya hau kan manyan turawan nan da sauran kasashensu, bala’in korona sun so ne ya ragargaji Nijeriya. Saboda haka Nijeriya karkashin kulawar Allah take, kullum cikin addu’a mu ke. A hanya a kasuwa, gida, masallatai, coci da sauransu duk addu’a mu ke yi. Don haka kai dan Nijeriya don neman daraja a wurin Turawa sai ka dauki bakin fenti ka shafawa kasarka saboda wata muguwar bukatarka, wai a sake baka Nobel. Wannan Nobel da aka ba ka da za mu bayyana bayaninka a turai su sanka da ba ka sake motsawa a Nijeriya ba. Saboda muna da cikakken bayani kan yadda lamurran suke. Na farko ba ka san siyasar Nijeriya ba, sai dai gaba da raini da kin ci gaban Nijeriya da Soyinka ke fama da su.
Saboda haka duk yadda suke nufin Buhari ya wuce nan, kuma duk yadda suke son Buhari ya samu matsala, don idan ya samu matsala ai gabadaya ‘yan Nijeriya ne suka samu matsala. Don wallahi ba don Korona da zuwa yanzu Buhari ya kammala kudurorinsa na gyaran Nijeriya. Wannan kuma hatta sauran kasashen duniya, sai da tattalin arzikinsu ya tabu. Ko ina an shiga wani hali. Allah ya dauke wannan cuta daga Nijeriya da duniya ma gabadaya. Da yardar Allah kafin 2021 da yawa masu surutun nan sai sun ji kunya. Kuma yanzun ma inshaAllahu rabbi sai sun yi shirun.
Saboda haka ina kira ga ‘yan kwadago da su tuna Nijeriya kasarsu ce, ku rika cizawa kuna hurawa. ‘Yan siyasa suna shiga cikinku suna so su yi amfani da ku, Abin da ya shafi siyasa wanda wani mai waka na MTN yana cewa, Rabbana ka nuna mana gaskiya, son kudi zai sa ka sha wuya, ka daura wuka bisa kan wuya, inka yanka sai ka sha wuya, daga baya anai maka dariya, kai ne wawa Nijeriya. Wani mutum da ya yi wakar rabbata nuna mana gaskiya. Saboda haka kada mu ki bin karatun wancan don yana mawaki, mu sanya wuka kan wuyanmu mu ciza mu hura, wannan tsanani duk kasar da ka sani ta duniya ya shafe ta. Kuma kowacce kasa tana ta kokarin ta ga yaya za a yi ta fid da kanta daga cikin wannan hali. kowanne dan Nijeriya sai ya bayar da gudummawarsa. Tilas sai an dafa an yi hakuri, watakila zai zama nan da dan wani lokaci za mu samu kanmu,
Me za ka ce daga karshe?
Allah Ya hana zagin shugabanni, kuma akwai aya akan haka. Shugabanni ko ba ma na musulmi ba ne. Shugaban da ba ka so sai ka jefa kuri’a ka hana shi cin zabe. Idan kuwa ya ci zabe sai ka janye saboda kasarka. Saboda haka a nan dan Nijeriya duk da Soshiyal midiya kullum ana yada farfagandar makiya Nijeriya, toh ni ina goyon bayan gwamnatin tarayya kan duk wanda aka kama da kokarin hada irin wannan fitina a hukunta shi hukunci mai tsanani.
Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply