Kannywood: Fati Washa Ta Lashe Kyautar Gwarzuwar Jarumar Hausa A Birtaniya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Fatima Abdullahi da ake kira Fati Washa ta lashe kyautar gwarzuwar jaruman Hausa a wani kasaitaccen bikin fina-finan Afirka da aka gudanar a Birtaniya.

An sanar da Washa ne a matsayin gwarzuwar jaruma a taron karrama ‘yan Fim da aka gudanar ranar Asabar a birnin London.

Bikin wanda ake kira Afro Hollywood Awards ya shafi karrama jaruman fina-finan harsunan Nijeriya guda uku Hausa da Yoruba da Igbo da kuma na Inglishi a sassan kasashen Afirka,

Fati Washa ta lashe kyautar ne saboda rawar da ta taka a Fim din ‘Sadauki.’

Jarumar ta doke Aisha Aliyu Tsamiya a Fim din da ta fito “Jamila” da kuma Halima Yusuf Atete da ta fito a “Uwar Gulma”

Rahama Sadau ta wallafa hoton bidiyo a shafinta na Instagram, lokacin da Washa ta ke karbar kyautar, inda ta bayyana farin cikinta da godiya.

Washa ta ce ta sadaukar da wannan kyautar ga masoyanta tare da gode ma su, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook da ba a tantance ba.

Share.

About Author

Leave A Reply