Karin Mutum 1,867 Sun Kamu Da Cutar Korona A Nijeriya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar kula da yaduwar cututtuka, NCDC ta bayyana cewa, an samu karin mutum 1,867 da suka kamu da cutar korona a Nijeriya a halin yanzu, wadanda suka kamu da cutar sun kai mutum 107,345 kenan gaba daya a fadin tarayyar Nijeriya.

Hukumar ta bayyana wannan jimillar ne a shafin ta na tiwita ranar Juma’a.

Ta kuma kara da cewa, mutum 8 sun mutu a cikin awanni 24 da suka gabata. A halin yanzu wadanda cutar ta kashe sun kai 1,413 ke nan.

Cibiyar ta kuma ce, jihohi 23 tare da yankin babbar birin tarayya Abuja ne suka samar da adaddin wadanda suka kamu da cutar a wannan karon.

Bayanin ya nuna cewa, jihar Legas nada mutum 713 Filato na da 273; Babban Birnin Tarayya na da 199; Kaduna, 117; da Oyo, 79.

Haka kuma Enugu-58, Ondo-53, Kano-49, Sokoto-43, Ogun-37, Osun-37, Nasarawa-36, Ribas 28, Binuwai 24, Delta 24, Neja 24, Gombe 18, Edo 15, Taraba-12, Bayelsa-10, Ekiti-9, Borno-6, Zamfara-2 da kuma jihar Jigawa 1.

Cibiyar ta kuma ce, mutum 705 sun samu sauki cutar kuma tuni aka salami su zuwa gidajen su a fadin tarayyar kasar nan, a halin ya zu wadanda ska samu sauki gaba daya sun kai mutum 84,535.

Share.

About Author

Leave A Reply