Karin Mutum 317 Sun Kamu Da Cutar Korona, Inji NCDC

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar kula da cuttua masu yaduwa NCDC ta bayyana cewa, an samu karin mutum 317 da suka kamu da cutar korona a ranar 23 ga watan Yuli, hukumar ta sanar da haka ne a shafinta na intanet da safiyar ranar Asabar.

An kuma lura da cewa, cutar na karuwa a kulum a cikin mako tara da suka wuce abin da ke kuma nuna cewa, an shiga yaduwar cutar mataki na uku kenan musamman ganin yadda aka samu bullar nau’in cutar da aka lakaba wa suna ‘DELTA VARIANT’ a wasu sassan Nijeriya.

NCDC ta kuma ce, yanzu kenan wadanda suka kamu da cutar a fadin kasar nan su kai mutum 170,623 yayin da kuma mutum 2, 131 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.

Share.

About Author

Leave A Reply