Kasa Ɗaya Ko Zaman Kaskanci Ga Arewa?

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Duk masu bibiyar yadda abubuwa ke sauyawa a cikin kasar mu Nijeriya ba tare wani dogon hangen nesa ba, ya san zaman Nijeriya kasa daya kawai a baki ne ba a aikace ba.
A duk rana babu abubuwan dake fitowa daga jaridun Kudancin Nijeriya da sauran kafafen yada labarai na zamani sai zafafan kalamai, zage zage da cin mutunci daga masu fafutukar kafa kasar Biyafara da Oduduwa.
A kwanannan Gwamnonin Kudancin Nijeriya sun fitar da wata sanarwar bayan taro akan sake tsara yadda ake tafiyar da al’amurran Nijeriya musamman harkar da ta shafi rabon arzikin kasa da ake kira da ‘restructuring’.
Idan mukayi duba a baya bayan nan zamuga cewar tun kafin zanga zangar lumana ta ENDSARS mutanen arewacin kasar nan dake zaune a kudanci suke fuskantar tsangwama, kisan gilla, wawashe da kuma kona dukiyar Yan-arewa wanda ya zama ruwan dare a, kudancin Nijeriya.
Shirya zanga zangar ENDSARS kusan ta budewa, Yan-Kudancin kasar nan wata kafa ta inda suke cin karen su babu babbaka wajen cin zarafin Yan-Arewa.
Halin da muka sami kan mu tabbas muna cikin kaskanci a zamantakewar mu ta kasa daya al’umma daya. Bayan anyi zanga zangar ENDSARS an karkashe Yan-Arewa, an kona masu motoci, da dukiyoyin su. Amma duk a arewacin Nigeria babu wanda yayi kokari kamar tsohon Gwamnan Sokoto Mai-Girma Alhaji Dalhatu Bafarawa wajen tattara bayanan illar da a kayiwa mutanen mu.
Bayan wannan kokari na Bafarawa babu wani abu da, aka yi da zai karfafawa Yan-arewa gwiwwa da cewar suma Yaya ne. Sai gashi yanzu ana biyan diyya ga wayanda sukayi asara a lokacin wannan zanga zangar ENDSARS, amma babu mai maganar Yan-Arewa.
Sai gashi kuma Gwamnonin kudu sun yi wata haduwa akan sake fasalin kasar nan.
Duk wani Dan-Arewa yasan cewa a yanzu mun zama shara kome sai a zo a, zubar a kan mu mun zama mune almajirai, cima zaune, marassa alkibla da dai sauran kalamai na batanci.
Hakika babu abunda yafi zame mana alheri da mafuta face a raba kasar nan kowa ya kama gaban sa. Babu ko shakka Arewa da Yan-arewa mun sami dama fiye da ko wane yanki sai dai tun bayan kashe su Sardauna wayanda suka biyo bayan su maimakon su dora sai ya zama kawai babu abunda ya zama a gaban su shine rike madafun iko ba tare menene zasuyiwa Arewa ba wayanda yanbaya zasuyi alfahari da shi ba.
Babu abin da Arewa ke dogaro da shi face harkar noma da kiwo. Amma maimakon su dage wajen habaka noma, masana’antu, ilimi, lafiya da dai sauran abubuwan da zasu inganta rayuwar Yan-Arewa.
A yau idan muka dubi yadda al’amurran kasar nan ke tafiya mune koma baya ta kowane fanni. Idan muka dauki ma’aikatan gwamnatin tarayya, za mu ga cewar Yan-Kudu sun fi mu yawa nesa ba kusa ba, duk da cewar an kafa ma’aikata da za ta kula da raba dai dai wajen daukar ma’aikata. Raba Nijeriya zai bai wa mutanen mu damar samun guraben aiki su kuma babu ko shakka guraben su zasu zama masu karancin.
Idan muka dauki bangare bankuna da sha’anin kudi, za mu ga Yankudancin kasar nan sun mamaye ko’ina wanda idan aka raba Nijeriya bankunan kudu ba za su iya isar ma’aikatan su ba wanda zai haifar da rashin aiki a tsakanin su.
A bangaran masana’antu kuma, kusan dukkan kayan da ake sarrafawa a, Kudancin kasar nan sai an kawo su arewa ake sayar dasu. Wanda raba Nijeriya zai sa mu dawo cikin hayyacin mu wajen farfado da masana’antu da zasu habaka tattalin arzikin Arewa da samarwa matasa aiki ta yadda zai bamu damar mu sarrafa kayan mu kuma kuma mu sayar a cikin mu.
Idan muka dauki bangaren kiyon kaji da, akeyi a kudancin kasar nan basa iya cinye kwai da suke samarwa sai an kawo shi arewacin Nijeriya. Raba kasar kam tabbas wannan zai baiwa mutanen Arewa damar shiga harkar kiyon kaji da, shima zai habaka tattalin arzikin arewa da samarwa matasan mu aiki.
Sannan kuma a bangaren kasuwanci musamman wanda Igbo ke dashi to fadin kasar to yadda suka kafa kasuwar su a duk manyan garuruwa da kyayukan arewa wanda jarin su ya haura Naira Tiriliyan dari. Amma jarin Yan-Arewa dake kudu jarin su bai taka kara ya karya ba. Babu ko tantama kasuwancin Inyamurai zai samu tazgaro. Kuma wannan zai karawa mutanen mu damarmakin shiga kasuwanci.
A yanzu dai lokaci yayi da dukkan Yan-Arewa zasu tashi haikan wajen kin amincewa da sake tsara yanayin zamantakewar mu, mu nemi a raba kasar nan domin ko muna so ko bama so Nigeria sai an raba ta. Kuma ga dukkan alamu sauran bangarorin kasar sun yi nisa wajen kama hanyar ballewa daga Nijeriya, amma mu Yan-Arewa mun zauna mun daga sai mu mun zauna da mutanen da basa kaunar zama damu.
Idan manyan mu na Arewa sun yarda da zaman kaskanci kullum ana cin mutuncin mu, addinin, al’adunmu da yankin mu baki daya. Da zaman mu Yan Nijeriya kullum cikin kaskanci saboda jiran kason kudin mai, gara rayuwar yanci da dogaro da kan mu.
Ra’ayin:

Ado Umar Lalu
Shamsu Mohammed Funtua
Lawal Saminu
Lawal Sani Usman
Umar Sani Lalu.

Share.

About Author

Leave A Reply