Kasar Argentina Za Ta Fara Rigakafin Korona A Shekarar 2021

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kasar Argentina ta sanar da cewa zai yiwu ta fara amfani da rigakafin cutar Korona na Kasar Rasha a farko-farkon shekarar 2021.

Shugaban Kasar Argentina Alberto Fernandez ne ya sanar da haka a yau Laraba a wata hira da ya yi da ‘yan jarida. Shi dai wannan rigakafi na Kasar Rasha sunansa Sputnik V

Tun a ranar 6 ga watan Nuwamban wannan shekara ne dai shugaban na Argentina ya cimma yarjejeniyar samun rigakafin guda miliyan 25 daga Shugaba Vladimir Putin na Rasha. Inda a hirar su ta wayar tarho Putin ya tabbatarwa da Fernandez cewa a karshen wannan shekara za su aika wa Argentina da rigakafin.

A sanarwar tasa, shugaban na Argentina ya ce, suna ci gaba da aiki kafada da kafada da Kasar Rasha don ganin an fara wannan rigakafi a farkon shekara mai kamawa ta 2021.

Share.

About Author

Leave A Reply