Kirkirarrun Karairayin EFCC A Shari’arta Da Diezani Da Dauda Lawal

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Abba Yahaya Sulaiman

Ya zamar mana wajibi ne mu fitar da wannan sanarwar manema labarai, duk da cewar mu ba ma’aikatan Dauda Lawal ba. Amma, a matsayinmu na nagartattun ‘yan Nijeriya wadanda ke da burin ganin bunkasar Nijeriya. Kuma wadanda suka yi suka yi amannar cewa, ya kamata hukumomi irin EFCC wadanda ake daukar dawainiyarsu da gumin talaka, su kasance masu kare muradin talakawa, ya kamata su kasance masu yin komi bisa gaskiya da amana.

Wannan takardar tamu mun yi ta ne a matsayin martani ga sanarwar da EFCC ta yi na kalubalantar labaran da suka yi yawo na cewa ta janye karar da ta shigarda Diezani Allison Madueke, Ben Otti, Nnamdi Okonkwo, Lanre Adesanya da Stanley Lawson. Inda hukumar ke kokarin rudar jama’a akan lamarin da ya wakana a gaban kotu, kuma jaridun Nijeriya suka nakalto. Kokarin EFCC shi ne son nuna abin da ya sa ta kori kararrakin dukkanin sauran mutanen da take zargi amma ta bar sunan Dauda Lawal a matsayin wanda ake zargi shi kadai tilo.

Ga masu bibiyan wannan shari’ar tun daga farkonta za su fahimci cewa Hukumar EFCC ba ta da niyyar gabatar da daya daga cikin mutanen da take zargi a kotu, muradinta kawai shi ne cin mutunci da neman wulakanta Dauda Lawal. Allah kadai ya san dalilin da ya sa EFCC kokarin bata mishi suna, kwace mishi dukiya da kadarorin da ya kwashe sama da shekaru 30 yana aiki kafin ya same su. Bai taba yin aikin gwamnati ba, don kuwa ma har sai da ya kai matsayin Babban Darakta a shahararren bankin ‘First Bank’.

Kamar yadda jaridu suka nakalto wannan labarin, lamarin ya samo asali tun a shekarar 2016, lokacin da EFCC ta kama Dauda Lawal ta tsare shin a tsawon makonni saboda kawai wata cinikayya da ya gudanar a aikinsa lokacin yana Darakta a ‘First Bank’. Tun a wancan lokacin Dauda Lawal ya bayyana rashin hannunsa a duk wani zargin badakala, tare da shirin kare kansa a gaban kotu. Sai dai abin da Dauda Lawal bai sani ba, ashe ana kokarin a wanke asalin wadanda ma ake zargi a shari’ar ne, tare kuma da yunkurin bude sabon fagen zaluntarsa, tunda wannan ba dai matakan shari’a ba ne ake bi.

A takardar sanarwar manema labaranta, EFCC ta yi ikirarin cewa ta sallami dukkanin sauran wadanda ake zargi tare da ci gaba da shari’a da Dauda Lawal, wanda sun manta mataki ne da suka dauka a gaban kotu, sannan kuma hukumar ta ki sanar da cewa, a dukkanin mutanen da take zargi a shari’ar, Dauda Lawal ne kawai ke halartar zaman kotun, bai taba fashin zuwa ba. Kuma hukumar ta EFCC ce fa da kanta ta taba sanarwa cewa, duk sauran wadanda ake zargi a shari’ar sun sha kawo uzurori don su kaurace ko kawo tsaiko ga shari’ar, amma duk da haka suka dauki matakin wanke su ta hanyar korar karar da suka shigar da su, amma kuma wai ta ci gaba da shari’a da mutumin da bai taba fashin halartar zaman kotu ba, wannan ma ai abin dariya ne.

Saboda haka, muna so a san cewa, dukkanin wadanda ake zargi ciki har da wadanda aka ce an kori kararsu sun halarci zaman kotu na ranakun 24 ga watan Mayun 2019 da ranar 5 ga watan Nuwamban 2019, amma babu wanda a cikinsu aka zarga da kawo cikas ga shari’a, sai dai ma aka ce wai an kori shari’arsu. Kai ka ce, ba EFCC din ba ne da kanta ta zarge su da kokarin kawo cikas ga shari’ar.  Idan har da gaske EFCC ta raba shari’ar ne, toh mene ne kuma ya sa ta shigar da wasu gyararraki a shari’arta da Dauda Lawal, ba tare da ambaton sauran wadanda ake zargi ba – ya kamata dai su fadi gaskiya kan wannan lamarin.

Haka kuma, madogararmu ita ce rahotannin jaridun da suka nakalto cewa EFCC ta janye karar da ta shigar da Diezani da Otti, kamar yadda yake rubuce a takardar shari’ar, wanda ke dauke da sunan Dauda Lawal kawai. Muna kalubalantar Hukumar EFCC da ta wallafa takardar karar don ta musanta abin da muka fadi. Idan EFCC ta ce, har yanzu shari’arta da Diezani, Okonkwo, Lawson, Adesanya da Otti tana nan, muna kira gare su da su nuna mana takardar shari’ar. Ai ko dalibin ajin farko a sashen koyon shari’a ya san cewa, duk wanda aka ayyana ya gudu, ba a gudanar da shari’arsa har sai an samo shi.

Shawararmu ga EFCC ita ce, su waiwayi dalilin da ya sa aka kafa su, don su gudanar da ayyukansu ba tare da nuna wariya, son rai da tsana a yaki da cin hanci da rashawa. Farautar mutane ba tare da dalili ba, bin son rai da nuna wariya a mu’amala da wadanda ake zargi alamu ne da ke nuni da cewa sun sauka daga ainihin dalilin da ya sa aka kafa su.

Dangane da lamarin Dauda Lawal kuwa, mutum ne nagari kuma samfuri abin koyi ga matasan arewa. Mun san cewa ko ba dade ko ba jima gaskiya za ta yi halinta. Ga jama’a, muna sanar da su cewa za mu ci gaba da bin diddigin lamarin nan tare da sanar da hakikanin abin da ke faruwa.

Sa Hannu:

Abba Yahaya Suleiman,

A madadin: NORTHERN YOUTHS IN DEFENCE OF DEMOCRACY AND JUSTICE

Share.

About Author

Leave A Reply