Kiwon Lafiya Da Cututtuka A Mahangar Ilimin Kimiyyar Zamantakewa ‘Sociology’ (1)

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A shekarun baya idan aka yi maganan cututtuka a na danganta su ne kaitsaye da bangaren kiwon lafiya na kimiyya, rashin lafiya kuma a na danganta ta ne da wani bayyanannen alama a jikin mutum na cewa ya na fama da cuta. Haka kuma a wancan lokacin samar da magani ga cututtuka sun takaita ne kawai ga shan magunguna ko kuma a yi wa mara lafiyan aiki (Surgery). Saboda wannan dalilin ne ya sa idan a na son fahimtar cuta yadda ya kamata, sai dai a yi nazarin wanda ke dauke da cutan.
Sakamakon ci gaba da a ka samu a fannin kimiyya da fasaha ne ya sa duniya ta ci karfin tunanin mutane a kan kiwon lafiya da cututtuka. Wanda a da mutane idan ba su da lafiya, sai su alakanta cutar da wani zunubi, ko kuma annoba, ko kuma wani lakani na Kakanni. Amma a sakamakon ci gaban, sai ya zama yanzu idan mutum ba shi da lafiya, ya kan nufi asibiti ne domin likita ya duba shi.
Wannan ci gaba da kimiyya da fasaha su ka kawo a fannin kiwon lafiya ne ya sa a kasashen da su ka habbaka (Debeloped Nations) ta kai ga an kawar da wanzuwar wasu cututtukan da a ke iya dibansu a lokacin mu’amalar yau da kullum. Sai dai a makwafin irin wadancan cututtuka, sai ya zama an samu wasu sabbin cututtuka wadanda su ne ke zama sanadin mutuwar al’umma. Irinsu cutar Kansa, Ciwon Suga, Kanjamau, da hadarin mota ko abin hawa, da dai sauransu.
Idan mutum ya kalli wasu daga cikin wadannan sababbin cututtukan da na bayyana a sama, zai iya fahimtar wani abu da su ke kamanceceniya da juna a kai, ko kuma in ce akwai wani sanadi guda daya da ke janyo su. Wannan sanadin shi ne yanayin yadda mutum ya ke tafiyar da rayuwarsa ‘Life – style’. Kenan harkar kiwon lafiya da cututtuka ta fi karfin a takaita ta ga wani bangaren ilimi guda daya. Dole ne a na bukatar a fahimci me ke janyo cututtukan, shin sababbin cututtukan nan na da alaka da yanayin tunanin mutum? wanne gudummawa al’umma ke bayarwa ga mutum wurin kamuwa da cututtukan nan? Wanne tsarin rayuwa ya kamata mutum ya bi domin kaucewa wadannan cututtuka?
Wadannan tambayoyi da wasu da dama ne su ka samar da sabon fanni a ilmin zamantakewa da sanin halayyar jama’a (Sociology) wanda a ke yi wa lakabi da ‘Medical Sociology’. Ma’ana bangaren ilmin sanin halayya da zamantakewa da ke nazarin kiwon lafiya da cututtuka. Shi wannan bangare na ilimi aikinshi shi ne binciken yanayin yadda a ke gudanarwa da tafiyar da al’amarin kiwon lafiya, da kuma yadda a ke kallon cututtuka. Wannan bangaren ilimin ya na binciken alakar likitoci da marasa lafiya, da kuma lokacin da zai yiwu a iya yi wa mara lafiya uzuri da lokacin da ba zai yiwu a yi mishi uzuri ba. sannan bangaren ilimin kan yi bincike a kan magunguna da tasirinsu, da kuma ra’ayoyin masana halayyar jama’a da zamantakewa dangane da kiwon lafiya da cututtuka.
Bayan samuwar wannan fannin, matsalar farko wacce tuntuni dama akwai ta a fannin kiwon lafiya da cututtuka ita ce ta samar da wani tsayayyen fassarar me a ke nufi da wadannan abubuwa; Lafiya da Cuta. Wanene mara lafiya? Wanene mai lafiya? Shin rashin lafiya na nufin samuwar cuta? Shin cuta na da bambanci da rashin lafiya? A sharar fage ga wannan bangare na ilimi sai da a ka fara samar da bayani ga wadannan tambayoyi wadanda a baya babu cikakken bayani a kansu.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fitar da wani fassara kan mene ne lafiya. Inda a shekarar 1977 ta ce, lafiya shi ne wani yanayi na cikakken kuzarin gangan jiki, kwakwalwa, da kuma wadatuwa a mu’amalolin rayuwa, ba wai kawai rashin samuwar cuta ko kuma samuwarta ba.
Wannan fassarar ta hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fuskanci raddi da martani ta bangarori da dama. Saboda a bayaninsu ya na nufin kenan babu yadda za a yi a samu wani mutum mai lafiya a wannan duniyar, sai dai ko a wata duniyar. Cikakken kuzarin gangan jiki da kwakwalwa da kuma wadatuwa da mu’amalar rayuwa wasu abubuwa ne da ba za su yiwu ba. ko ba komi dabi’ar damuwa ma ta ishi mutum, haka kuma ga tunani wanda zai kawo nakasu ga cikakken kuzari ga kwakwalwa. Da wannan kadai za mu iya cewa babu wani gamsasshen fassaran abin da a ke nufi da lafiya.
Kafin na ci gaba da bayani zan so na yi karin haske dangane da wasu abubuwa guda biyu, su ne alamomin cuta (Symptoms) da kuma bayyanar cutan (Signs). Wadannan abubuwan biyu su na da bambanci. Na farko a na gane bayyanar cuta (Signs) ne ta hanyar gani da ido, misali ko a jikin fatar mutum, ko kuma idan a ka auna jininshi. Ita kuma alamar cuta (Symptoms) ba a iya gane ta da ido, sai dai shi mara lafiya ya yi wa likita bayanin abubuwan da ke damunsa, kamar misali mutum ya rika jin jiri na dibansa, da sauransu.
Ba a karin haske dangane da bambancin alamomin cuta da bayyanarta kawai zan tsaya ba, akwai kuma wani karin bayanin dangane da cuta, ciwo, da kuma rashin lafiya. Wadannan abubuwa guda uku bayaninsu shi ne ke kan gaba wurin bayyana bambancin da ke tsakanin kiwon lafiya da kuma sabon bangaren ilimi na ‘Medical Sociology’.

Awesome
  • User Ratings (2 Votes) 6.3
Share.

About Author

Leave A Reply