Kiwon Lafiya Da Cututtuka A Mahangar Ilimin Kimiyyar Zamantakewa (SOCIOLOGY) 2

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

(Ci gaba…)

Ba a lamarin karin haske dangane da bambancin alamomin cuta da bayyanarta kawai zan tsaya ba, akwai kuma wani karin bayanin dangane da cuta, ciwo, da kuma rashin lafiya. Wadannan abubuwa guda uku bayaninsu shi ne ke kan gaba wurin bayyana bambancin da ke tsakanin kiwon lafiya da kuma sabon bangaren ilimi na ‘Medical Sociology’.

Idan a ka yi maganan Cuta (disease), a na nufin wani abu wanda ya sabbabawa gangan jiki ko wani bangare na jikin mutum sauyawa daga yanayin da ya kamata ya kasance na koshin lafiya. A na gane cuta ne ta hanyar alamomin cuta ko kuma bayyanar cutan.

Ciwo kuwa ya na nufin wani hali da mutum zai tsinci kanshi na jin ba dai dai ba a jikinshi ko wani bangare na jikin nashi. Ciwo kan fara daga yanayin yadda mutum ke jin zafi, damuwa, da kuma rashin sakewa a al’amuransa na rayuwa. Babban bambanci a tsakanin cuta da ciwo, shi ne ita cuta ta kan bayyana kowa ya iya ganin alamominta ko bayyanarta a jikin mutum, idan an ga me fama da wata cuta a na iya cewa wancan cuta kaza c eke damunsa, saboda ga alamominta nan a tattare da shi. A yayin da Ciwo kuma wanda ke fama da ciwon ne kadai ke jin radadin abin da ke damunsa. Ba dole ba ne sai ya zama ciwon ya bayyana ko an iya ganin alamominsa. Matukar mutum zai rika jin wani bangare na damunsa, shi kenan ya zama wanda ke fama da ciwo.  Haka kuma don akwai cuta a tattare da mutum ba ya nufin mutumin nan na fama da ciwo ba ne.

Misali a nan, za a iya samun mutum da cutar kanjamau, zai yiwu alamomin cutar su bayyana na cewa ya na da cutar bayan an yi gwajin asibiti. Amma shi wannan mai cutar kanjamau ba ya jin wani ciwo a jikinsa, garau ya ke jinsa ba tare da wani radadi ba. Irin wannan ya na nuna cewa mutumin mai cutar kanjamau ya na fama da cuta ne ba ciwo ba. har sai zuwa lokacin da wannan cuta ta yi kamari tukunna, sannan ne mutumin zai tashi daga mai fama da cuta zuwa wanda ke da ciwo.

Haka nan a daya bangaren, za a iya samun mutum ya na fama da ciwo amma kuma babu wata cuta a jikinsa, ya na yiwuwa sosai ma. Sai ka ga an je asibiti an yi ta gwaje gwajen neman cutar da ke sa mutum jin ciwo a wani bangare na jikinsa amma a rasa samunta. Mutanen da ke fama da ciwon ‘Myalgic Encephalomyelitis’ suna jin zafin ciwon, amma idan an gwada ba a ganinsu da wata cuta a tattare da su.

Bayan bayanin bambance bambance da ke tsakanin cuta da ciwo, akwai kuma bambanci tsakanin wadannan abubuwa biyu da RASHIN LAFIYA. Rashin lafiya ba kawai ya na nufin kasantuwar cuta ko fama da ciwo ba ne, hadakar duka biyun ne ke samar da rashin lafiya. Rashin lafiya ya na nufin wani yanayi da mutum zai tsinci kanshi a wani yanayi wanda ba zai iya gudanar da al’amuran rayuwarshi kamar yadda ya saba gudanar da su ba sakamakon wata cuta ko ciwon da yak e fama da shi.

Bambanci a tsakanin ciwo da rashin lafiya shi ne yanayin yadda al’amarin ya yi kamari. A yayin da mutum ke fama da ciwo shi kadai abin ya shafa, saboda ya na iya fita kasuwa ko zuwa wasu uzurorinshi. Amma idan mutum na fama da rashin lafiya, hakan na iya shafar mutanen da ya ke rayuwa tare da su. Ba zai iya zuwa kasuwa ba, ba zai iya ci gaba da gudanar da al’amuransa na yau da kullum ba.

Sakamakon rashin lafiya na shiga cikin mu’amala tsakanin wanda ba shi da lafiyan da sauran al’umma ne masana ilimin kimiyyar zamantakewa suka mayar da hankali a kan kiwon lafiya da cututtuka. Saboda idan za a zura ido wata annobar cuta ta shigo ta addabi al’umma, zai zama yanayin tafiyar da al’amura sun samu matsala, ba kamar yadda a ka saba tafiyar da su ba.

Kamar yadda ya ke a ilimin na kimiyyar zamantakewa da sanin halayyar jama’a (Sociology), akwai mabambanta nazarori dangane da yadda mabambantan bangarori su ke kallon rayuwar zamantakewa. wadannan bangarori sun kasu gida uku, akwai; bangaren ‘Functionalism’, ‘Conflict’ da kuma ‘Symbolic Interactionism’.

Nazarin bangaren ‘Functionalism’ shi ne ya fara bayyana a ilimin, haka kuma shi ne ya fara yin nazarin kiwon lafiya da cututtuka. Wannan bangare ne wanda ke bayanin yanayin yadda gabadaya  al’umma ke gudanarwa, ta yadda kowanne bangare na al’umma zai rika bayar da nashi gudummawan domin a kai ga nasara, ba tare da wata tangarda ba. Alal misali, bangaren al’adu zai rika gudanar da aikinshi na tabbatar da ci gaban al’ada da wanzuwarta, bangaren addini kuma zai rika hada kan mabiya domin karfafa imaninsu, bangaren tattalin arziki kuma domin samarwa al’umma da abin masarufi, haka nan sauran bangarorin, irinsu gidan sojoji, iyali, makarantu da sauransu.

A sakamakon wannan tushe na bangaren ‘Functionalism’ ne ya sa nazarinsu ke kallon kowanne mutum a matsayin mai amfani a cikin al’umma, kuma wanda a ke bukatar gudummawarsa domin al’umma ta ci gaba da gudanarwa yadda ya kamata. Idan mutum ya kasance ba shi da lafiya, za ta yiwu magidanci ne, kuma ma’aikaci a wata ma’aikata. Idan rashin lafiyan ya kwantar da shi, ba zai yiwu ya iya fita zuwa ma’aikatarsu ba, hakan na nufin kenan babu wanda zai nemowa Iyalin gidansa abin da za su ci. A dalilin haka wannan nazarin ya ke ganin cewa dole ne a dauki mataki a kan al’amarin rashin lafiya.

A kokarin ganin ya samar da wani nazari mai amfani, masani Talcott Parsons ya samar da wani nazari wanda ya kira da ‘Sick – Role’, wanda shi ne nazari mafi amsuwa a ilimin kimiyyar zamantakewa bangaren kiwon lafiya da cututtuka ‘Medical Sociology’.  A nazarin Talcott Parsons, rashin lafiya wani abu ne wanda ba a so, wanda ya saba da ka’idar al’umma, ta yadda mutanen da su ke fama da rashin lafiyan za su rika aikata wasu dabi’un da suka saba.

Duk da cewa Talcott Parsons ya gina nazarinshi ne ta hanyar dubi ga al’umman Yammacin Turai, amma za mu iya ganin amfanin wannan nazari na ‘Sick Role’ a al’ummunmu da ba chan din ba. ya kasa nazarin gida hudu, sannan hudun sai ya raba su gida biyu. Biyun farko ya yi bayani dangane da ‘yancin da mara lafiya ke da shi, biyun karshe kuma ya yi bayanin nauyin da ya hau kan mara lafiya.

Akwai ci gaba

Awesome
  • User Ratings (2 Votes) 2.4
Share.

About Author

Leave A Reply