Kiwon Lafiya Da Cututtuka A Mahangar Ilimin Kimiyyar Zamantakewa (SOCIOLOGY) 3

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Ci gaba…
‘YANCIN DA MARA LAFIYA KE DA SHI
Duk mutumin da ke fama da rashin lafiya ya na da ‘yanci tare da samun kariya ta siffofi guda biyu. Na farko dole ne a yi mishi uzuri kan duk wasu mu’amaloli na rayuwa ‘Excuse From Social Responsibility). Wannan na nufin mara lafiya ba zai rika zuwa wurin aiki ba, ba zai rika yin wasu hidindimu ko daukar dawainiyar iyalinshi ba. hakan na faruwa ne ta fuskacin tsananin ciwon, da shi mutane ke iya fahimtar shin ya kai kiman da za a ba mutum wannan ‘yanci?
Na biyu daga cikin ‘yancin mara lafiya shi ne a na yi mishi uzuri daga dukkan zargi ko daura laifi. Saboda mara lafiya ya na kasancewa ne a cikin wani irin yanayi wanda ba shi da ikon fid da kansa har sai lokacin da sauki ya samu. Sannan duk abubuwan raki ko halin da damuwa da zai shiga, ba zai yiwu a ga laifinsa ba. saboda haka mara lafiya ya na da ‘yancin a kula da shi, sannan a ba shi duk wata gudummawa da ta dace.
SHARUDDAN TABBATAR DA RASHIN LAFIYA
Talcott Parsons ya ce mara lafiya ba zai samu wadancan ‘yancin ba har sai ya zama cewa ya cika wadannan sharudda guda biyu. Na farko shi ne, ya zama a na iya fassara yanayin da ya ke ciki a matsayin mawuyacin hali, ko kuma wanda a na ganinsa an san jikinsa ya yi tsanani. Ba kawai mutum ya kwanta ciwon kai ko wani karamin ciwo ba sai ya ki fita wurin aiki ya ce ba shi da lafiya. Sai ya zama mutum ya na cikin yanayin da bay a jin dadin komi saboda ciwon.
Na biyu cikin sharuddan shi ne, dole ne mara lafiya ya nemi taimakon likita domin samun lafiyan ciwon da ke damunsa. Ba kawai mutum ya kwanta a gida ba tare da wani kokari na ganin ya samu sauki ba. idan mutum babu wani yunkuri da ya ke yi don ganin ya samu sauki, za a kai lokacin da zai rasa wadanchan ‘yancin da a ka bayyana.
Wannan nazarin na Talcott Parsons ya samu kalubale sosai, saboda idan a ka ce za a bi wadannan matakai guda hudu wurin tabbatar da rashin lafiya ga mara lafiya, kenan kawai masu fama da matsananciyar cuta ne za a rika kallo a marasa lafiya. Sannan kuma sai likita ne kadai zai iya tabbatar da cewa mutum mara lafiya ne, ko da kuwa mutumin na jin ciwo na cinsa sosai. Haka kuma Talcott ya manta cewa ba kowa ne ke zuwa wurin likita ba yayin da ba shi da lafiya. Bangaren su Karl Marx su na kallon al’amarin kiwon lafiya a matsayin wata hanyar ci gaba da danne raunana da bunkasar tattalin arzikin masu kudi. A wurinsu masu kudi ne ke sarrafa magunguna, don haka su ke amfana idan mutane su ka kamu da cuta ko ciwo har zuwa siyan magani ko zuwa asibiti.
Nazari na biyu shi ne wanda ya samo asali daga nazariyyar makarantar ‘Conflict’ a wasu lokuta a na kiran wannan nazarin da Nazariyyar Siyasar Tattalin Arziki ‘Political Economy’. Wannan nazari ne daya bubbugo daga masani Karl Marx, duk da cewa a farko sun dace da ‘Functionalist’ a kan cewa an kirkiro kiwon lafiya ne domin saita lamurra da rayuwar al’umma, tabbatar da wanzuwar dokoki da oda.
Wannan nazariyyar ta Karl Marx ta samu bambanci ne da ‘Functionalist’ inda ya ke cewa al’amarin kiwon lafiya ba komi ba ne face wata kafa da ‘yan jari hujja ke cin karensu babu babbaka.
Masanin ya ci gaba da cewa ita kanta cuta da ciwo sun samo asali ne sakamakon zaluncin da a ke nunawa talakawa, tauye hakkinsu da rashin mutunta rayuwarsu. Saboda a kowacce al’umma ta kaso kasha biyu ne. akwai wadanda su ne a sama, ‘yan danniya, ‘yan jari hujja a daya bangaren kuma akwai ‘yan kasa, wadanda a ke dannewa, su ne kuma ma’aikata.
A wannan nazariyyar, sun ce an kirkiro kiwon lafiya ne domin ‘yan jari hujja su tabbatar da cewa ma’aikata ba su daina yin aiki ba. Saboda sai su na da koshin lafiya ne sannan za su iya yin aiki a ma’aikatunsu da masana’antu. Likitoci da asibitoci duk sun samu ne a kan samarwa da ma’aikatan koshin lafiya da kawar musu da cututtuka.
Haka kuma kiwon lafiya ke bambancewa tsakanin me kudi da talaka. Me kudi idan ya kamu da rashin lafiya, zai je asibiti mai kyau, mai kwararrun likitoci. Amma idan talaka ya kamu da irin makamanciyar wannan cuta, sai dai ya yi ta bin kananan asibitoci domin neman lafiya, wanda a karshe ciwon zai ci shi har mutuwa. Daga karshe nazarin ya tafi a kan cewa su masu kudi su ne ke cin ribar magunguna da asibitoci, saboda da kudadensu a ke zuba hannun jari a kamfanonin magani.
Daga cikin martanin da a ka mayarwa nazariyyar ‘Conflict’ akwai batun cewa sun rufe idonsu daga yin bayanin al’ummun da ba tsarin jari hujja su ke a kai ba. wannan martanin da a ka yi wa nazarin ne ya samar da nazariyyar ‘Interactionist’.
Nazariyyar ‘Interactionst’ shi ne nazariyya na uku a tsarin nazarorin da ke ilimin kimiyyar zamantakewa. Sun bambanta da sauran nazarorin da na yi bayani a baya. Saboda sun mayar da hankali ne a kan fahimtar daidaikun mutane, ba wai gaba daya al’umman ba. sun fara ne da binciken dalilan da ke sa mutum ya bukaci taimakon likita ko ya je asibiti a lokacin da ba shi da lafiya.
Haka kuma sun muhimmanta bincike dangane da irin mu’amalar da ke wankana a tsakanin likita da mara lafiya. Sun tafi a kan cewa abin da ke tabbatar da ciwo ko rashin lafiya ba kawai bayyanar cuta ba ne, a’a yanayin yadda al’umma su ka fassara menene cuta, ciwo da rashin lafiya da kuma menene lafiya. A na iya samun mutum wanda ke fama da gagarumar cuta, wanda hakan bai isa ya tabbatar da cewa shi wannan mutumin ya na fama da ciwo ba.
Wannan nazarin ya bayyana cewa mutum a kashin kansa ne ke iya bayyana cewa lafiyansa lau ko kuma ba shi da lafiya. Saboda kowanne al’umma akwai yanayin fassararsu na rashin lafiya. Sannan kuma mutum shi ne kadai ke jin wasu alamomi da za su iya gamsar da shi. ko da mutum ya samu tabbacin ba shi da lafiya, dole akwai bukatar wasu abubuwa wanda al’umma ne ke gina ma mutane su, na yadda za su ginu a dabi’ar zuwa wurin likita.
Kamar misali, a kauyukanmu da dama za ka tarad da mace ba ta da lafiya, mijinta kuma ya yi nisa. Amma ba zai yiwu ta fita ko a kai ta asibiti ba, har sai mijinta ya dawo ko an iya samunshi ya amince da a kai ta. Da yawa ma ba su yarda matarsu ta je asibiti ba, saboda sun dauka kaskanci ne ko kuma kaucewa al’ada. Musamman ma a al’amarin da ya shafi matsalar haihuwa, matsalolin da su ka shafi cututtukan al’aura da makamantansu. Al’adar ta gadarwa mutane da kin yarda matansu su haihu a asibiti saboda kaucewa likitoci maza. Wannan dogon nazari ne, wanda ke bukatar a dau lokaci mai tsawo a na yi. Sai dai kawai na gudanar da wannan ne a matsayin gabatarwa ga kiwon lafiya da cututtuka a mahangar ilimin kimiyyar zamantakewa.

Awesome
  • User Ratings (2 Votes) 5.8
Share.

About Author

Leave A Reply