Korona Ta Shiga Kurkukun Kaduna, Har Mahaifiyata Ta Kamu!

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Mohammed Ibraheem Zakzaky

Kwanaki hudu da suka gabata, bayan da likitocin iyayena suka ziyarce su kamar yadda aka saba, sai Mahaifiyata ta yi korafin cewa tana fama da tsamin jiki, zazzabi da daukewar jin kamshi ko wari. Jin haka ya sa likitocin yin wasu ‘yan gwaje-gwaje don su fahimci abin da ke damunta. Cikin gwajin da suka yi har da na cutar Korona. Yana da kyau a sani cewa, an hana mahaifiyata samun cikakken kulawar likitoci, domin kuwa tsawon shekaru kenan tana fama da azababben ciwon gwiwa.

Sakamakon gwajin cutar ya nuna mahaifiyata na dauke da Korona. Na yi mamaki matuka da har aka samu Korona a Kurkukun, musamman bisa la’akari da irin taka-tsantsan da ma’aikatan Kurkukun ke yin a kiyaye barkewar cutar. Saboda mu ma a namu bangaren mun yi ta bin dokokin kiyaye afkuwar irin haka, su ma kuma mahukuntan kurkukun suna yin nasu kokarin kan hakan.

Ko da na samu labarin sakamakon gwajin, sai da na bi duk wasu hanyoyi da suka dace don tabbatar da ingancinsa. A tsammanina hukumar kurkukun za ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta, ta hanyar sanar da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru el-Rufai cewa wannan annobar ta kama mahaifiyata Zeenah Ibraheem, kuma tana bukatar kulawar gaggawa a asibiti. Ba su aikata hakan ba, shi ya sa na ke yin bayani da kaina.

Ga bayanin cikakken halin da ake ciki:

RANAR DA SAKAMAKON GWAJIN YA FITO: An isar da wannan mummunan labari ga Mataimakin Kwanturola na Kurkukun, kai har ma da shi Kwanturola din. Shi ne ya bayar da cikakkiyar dama ga jami’an kiwon lafiya domin su bayar da kulawar gaggawa ga mahaifiyata, Zeenah Ibraheem.

RANAR FARKO: An ci zarafin wadannan jami’an kiwon lafiya. Wanda ya hana su bayar da taimakon gaggawa ga mahaifiyata kamar yadda suka kuduri aniya.

RANA TA BIYU: Sai aka sake bayar da oda ga Kwanturola na Kurkukun kan ya sake gudanar da gwajin Koronar. Gwajin da kwararru suka yi har sakamako ya tabbatar da tana dauke da cutar bai wadatar ba. Wai sai an sake. Hakan kuwa muka yi.

Daga ranar da sakamakon ya fito, abin da ya dace a yi bisa ka’idar kiwon lafiya shi ne:

1. Dole ne a gudanar da gwajin cutar ga wadanda suka yi mu’amala da mahaifiyata, Zeenah Ibraheem.

2. A dauki matakin bayar da taimakon gaggawa tare da gaggauta kwantar da wadanda suka kamu da cutar a asibiti.

3. Bukatuwar killace dukkanin masu dauke da cutar, domin a basu kulawa ta musamman. Mahaifiyata, Zeenah Ibrahim ba ta samu ko daya cikin wannan ba.

4. Gudanar da gwaji ga dukkan wadanda ta yi mu’amala da su domin a yi wa tufkar hanci. Kuma a tabbatar da yi wa masu cutar magani.

RANA TA UKU: Har zuwa wannan rana ba a kai mahaifiyata asibiti ba. Ya fi kama da ana son yin amfani da wannan cutar ta Korona ne domin a kashe ta.

Ina son yin wata tambaya a nan: Mene ne dalilin da ya sa aka ki kai mahaifiyata asibiti? Me ya sa ku ke yin haka?

Sanin kowa ne cewa, Korona tana bukatar daukar matakin gaggawa. Toh me ya sa wannan ka’idar kiyaye cutar ta Korona ba su amfani akanta da kanshi?

A nan da na ce, a kanta, ina nufin mahaifiyata Zeenah Ibrahim. Inda kuma na ce, a kanshi, ina nufin Mahaifina Sheikh Ibraheem Zakzaky.

RANA TA HUDU: Tunanin bin matakan gudanarwa, kamar yadda tsarin aikin kurkukun ya tanada. Yana da kyau shugabancin kurkukun su gane cewa ba sai sun dulmiya kansu cikin wannan danyen aikin kisan kai kamar yadda mutane ukun da suka faro ta’asar suka yi ba.

RANA TA BIYAR: Babu wani abu da zan iya tabukawa domin ceto rayuwar mahaifiyata wacce sakamakon gwaji ya tabbatar da tana dauke da cutar Korona.
Haka nan babu abin da zan iya yi, idan ta tabbatar Mahaifina ma yana dauke da cutar.

RANA TA SHIDA: Yau ake cika kwana shida tun bayan da na samu labarin barkewar annobar a kurkukun. Wannan fa ita ce Nijeriyar da aka haife ni cikinta, wannan ita ce Nijeriyar da aka yi wa kannena kisan gilla, wannan ita ce Nijeriya da kana ji, kana gani za a hana ka kula da lafiyar mahaifiyarka.

Wannan sam ba a abin wasa ba ne. Cutar dai ba za ta tafi da kanta ba, sai an yi magani. Kuma ba shifci ba ne, domin kuwa gwaji aka yi aka samu sakamako.

Har yanzu mahaifiyata tana cikin kurkukun Kadduna, ba a kai ta asibiti ba, ba kuma a bata wata kulawar gaggawa ba domin kula da lafiyarta.

Mohammed Ibraheem Zakzaky.

Share.

About Author

Leave A Reply