Korona: TETFund, Bogoro Da Muradin Samar Da Cibiyar Binciken Ilimi, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Babbar nasarar bunkasar fannin ilimi shi ne ya zama an iya magance matsalar tsarin bincike na ilmi. A dalilin haka ne ya sa aka samar da Hukumar TETFund a Nijeriya. Ba kamar a shekarun baya ba, a yanzu lokacin shugabancin Farfesa Elias Bogoro ya sauya hukumar daidai da wannan aiki da aka kafa shi dominshi.

A shekarr 1903 da 1911 mace ta farko da ta fara amsan lambar yabo kan gudummawar da ta bayar a fannin ilmi na Physics da Chemistry, wato Marie Curie. An ruwaitota tana cewa, “Babu wani abu a duniya da ya kamata a ji tsoronsa; sai dai ma a fahimcesa. Yanzu lokaci ne na fahimta, domin mu rage tsoro.”

Matsaloli irinsu barkewar annobar Korona da a yanzu take dagulawa al’ummar duniya lissafi za su ci gaba da addabar mutane lokaci bayan lokaci. Wannan yanayin da Nijeriya ke ciki ne ya tabbatar da cewa ana matukar bukatar fadada lamarin bincike. A bisa wannan, tun kafin barkewar annobar ta Korona, TETFund karkashin shugabanta, Bogoro ta samar da shirin tallafawa ilimi domin ta karfafa masu son yin bincike.

Fiye da sauran lokuta na baya, wannan zamani ne da ake bukatar bunkasa bincike domin a dakile duk wata annoba da ke fuskantar duniya. Kasar Madagascar, alal misali ta yi ikirarin cewa ta samar da maganin Cutar Korona, wanda ta samar ta hanyar yin amfani da masananta na cikin gida a kuma cibiyoyin bincikenta. Wannan shi ne dalilin da ya sa dole a jinjinawa shirin TETFund na bunkasa binciken ilimi ‘Educational Research Development’ wanda Farfesa Bogoro ya samar.

Shi wannan shiri ne da zai taimakawa Nijeriya wurin gaggawar bunkasa kamr sauran duniya a fannin ilimi. Babu ko tantama, Farfesa Bogoro ya dau turbar farfado da kudurin gwmanatin tarayya, wanda a kansa ne ta samar da Hukumar TETFund a shekarar 2004; a matsayin wata kafa da za ta dauki dawainiyar tallafawa masana a jami’o’I domin su bunkasa fannin bincike.

Wasu daga cikin fannonin da TETFund ta fi mayar da hankali akwai binciken da ke nemo mafita ga matsalolin kasa, a bangarorin da suka shafi Tsaron Ksa, Hadin kan kasa, zaman lafiya, ilimi da horaswa, Bunkasar tattalin arziki, noma, bunkasar fasaha, wutar lantarki da sauransu.

Shi wannan bincike makasudinsa shi ne a samar da yanayin da zai ciyar da makarantun gaba da sakandare gaba. Bincike ne da zai mayar da hankali akan dukkanin fannonin ilimi da ake da su. Tsarin wanda a turance ke yi masa take da ‘Intitution-based research (IBR)’ tabbas zai farfado da binciken kimiyya a jami’o’I da sauran makarantun gaba da sakandare.

Tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo da Farfesa Suleiman Elias Bogoro kan kujerar shugabancin TETFund a ranar 21 ga watan Afrilun 2019, wanda ya yi matukar sauya hukumar zuwa mataki na gaba.

Hukumar TETFund a yau tana murnar kasantuwar jami’o’in Nijeriya a sahun jami’o’in da ke gaba a duniya, saboda wadannan shekaru hudu an kwashe su ne wurin tallafawa makarantun gaba da sakandare a fannonin bincike. Da dama za ta bayar, da na kawo wsu daga cikin wadannan hanyoyi da TETFund ke bi.

Daya daga cikin abubuwan da Farfesa Bogoro ya mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da da’a yayin gudanar da bincike, kirkira da kuma lamurran bunkasa. Ya fara ne da fasa sashen bincike da bunkasa a hedikwatar hukumar TETFund, wanda ta nan ne ake lura da sa ido kan daukar nauyin bincike a makarantun gaba da sakandare.

Wasu masana sun tafi akan cewa, da a ce hukumar TETFund tun farkon assasata ta samu Babban Sakatare kamar Bogoro, da a yanzu an dade da samar da maganin Cutar Korona da ta addabi duniya. A dalilin haka ne ma ya dace a jinjinawa Shugaba Buhari da ministan ilimi, Malam Adamu Adamu bisa dawo da wannan masani kuma namijin farfesa a matsayin shugaban TETFund.

A burin hukumar na son horas da malaman jami’a, TETFund tana da tsarin bayar da tallafi domin zuwa karo karatu ga malamai a ciki da wajen Nijeriya. A karkashin shirin horas da malaman jami’a akwai malamai 24,194 wadanda ke karatun digiri na biyu da na uku a jami’o’in kasashen waje.

Jami’o’i da malaman jami’a cike suke da murna da farin ciki da nasarorin da Bogoro ke samu. Ya dawo da martabar hukumar daga halin da ta shiga a shekaru biyu da ya zama baya nan.

A hade, a zamaninsa na farko da wannan na biyun a Hukumar TETFund, Bogoro ya yi kokari wurin ganin an yi komi bisa ka’ida kuma ingantacce a fannin makarantun gaba da sakandare. Za a iya ganin misali a jami’o’in Arewa maso yammacin Nijeriya.

Aikin raya makarantun gaba da sakandaren Hukumar TETFund a karkashin Farfesa Bogoro ya zagaye ko ina a fadin Nijeriya. Misali mu duba Arewa masu yamma a matsayin zakaran gwajin dafi. Duk da matsalar tsaro da yankin ke fama da shi, a shekarunsa uku a Hukumar TETFund, Farfesa Bogoro ya yi gine-gine muhimmai a Jami’ar Modibbo Adama dake Yola.

Haka kuma ya yi aikin gine-ginen dakunan karatu dalibai masu diban mutum 250 a Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Mubi, ciki kuwa har da ofisoshin malamai. Haka ma a Kwalejin Kimiyya Da Fasaha ta Idris Alooma dake Geidam Jihar Yobe an gina musu sashe sukutum na kimiyyar kere-kere.

Sannan a Kwalejin Ilimi ta tarayya dake Azare Jihar Bauchi, Hukumar TETFund ta gina dakin kwanan dalibai mata, dakunan karatu. A Jami’ar Maiduguri kuwa Hukumar TETFund ta gina sashen hukumar gudanarwa ‘Senate Building’, gidajen manyan malamai, fadada kai wutar lantarki, gina burtsate guda tara, manyan motoci guda biyu da dai sauransu.

Haka ita ma Jami’ar ATBU ta samu tagomashin sanya mata injin janareto guda uku, biyu masu karfin 800KVA, biyu masu karfin 500KVA, biyu masu karfin 100KVA domin amfanin jami’ar. Sannan kuma Hukumar TETFund din ta gyara dakunan kwanan dalibai da ofisoshin malamai.

A Jami’ar Jihar Taraba kuwa Hukumar TETFund ta yi gine-gine ciki har da kayan asibiti da motoci. Haka ma Jami’ar Tarayya ta Wukari dake Jihar Taraba ta samu tagomashin ayyuka daga Hukumar TETFund.

A saboda haka ne, Sanata Binta Mashi wacce ita ce shugabar kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin TETFund, ta ce lallai hukumar ta TETFund karkashin Farfesa Bogoro ta cancanci duk wani yabo da jinjina.

– Ibrahim shi ne Daraktan Sdarwa da tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC).

 

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply