Kotu Ta Bayar Da Umarin Kulle Dan Kasuwan Da Ake Zargi Da Kwacen Fili A Abuja

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A ranar Talata ne kotun Majastare da ke unguwar Wuse, Abuja, ta fara shari’ar wani Dan kasuwa mai suna Owolabi Akeemana wanda ake zargi leaven fili a Abuja

 

‘Yan sanda sun tuhumi Akeem da laifin barna da kuma keta doka.

 

Alkalin kotun Mr Eri ya kuma dage sauraron karar har zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu, domin sauraren karar.

 

Tun da farko, lauya mai shigar da kara, ASP Peter Ejike ya fada wa kotun cewa Dokta Anebi Lawrence, ya shigar da karar wani lokaci tsakanin shekarae 2005 da 2006 inda ya sayi wasu filaye biyu da ke unguwar Kubwa, Abuja.

 

Mai gabatar da karar ya ci gaba da cewa wanda ake zargin, Akeem da wasu mutum biyu, wanda a halin yanzu ba a kai ga kama su ba halin yanzu suun lalata shingen, suka kutsa kai cikin filin.

 

Laifin, in ji shi, ya ci karo da tanadin sashe na 97, 328 da 348 na dokar Penal Code.

 

Wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.

Share.

About Author

Leave A Reply