Kotu Ta Ci Tarar Wani Dan Damfara Naira 250,000 A Abuja

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wata  kotun tarayya da ke zama a Kubwa, yankin babbar birnin tarayya Abuja ta umarci wani matashi mai shekara 26 mai suna, Adebayo Samuel, wanda aka samu da laifin damfarar wata mata Dala $500 da ya biya tara Naira 250, 000.

Da yake yanke hukuncin, Alkali Bello Kawu, ya gargade shi da ya zaman mutum kirki a harkokinsa.

Tun da farko mai gabatar da kara, Dauda Ajadosu, ya nemi alkalin ya yi masa afuwa saboda nuna nadama da ya yi a yayin da ake gabatar da shari’ar.

“Samuel ya halarci dukkan zaman da hukumar EFCC ta kirasa ya kuma yi nadamar abinda ya aikata.

” Ina rokon kotu da ta yanke masa hukuncin tara saboda ya koma cikn al’umma don cigaba da gudanar da rayuwarsa, ” inji Ajadosu.

Share.

About Author

Leave A Reply