Kotu Ta Daure Magidanci Wata 18 A Gidan Yari Bisa Safarar Wiwi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A ranar Laraba ne kotun tarayya da ke garin Jos ta yanke wa wani magidanci mahaifin yara 15, mai suna Sunday Danladi hukunci zama gidan yari na tsawon wata 18 bayan da aka same shi da laifin safarar miyagun kwayoyi mai nauyin kilogram 18

Mai shari’a Justice Dorcas Agishi, ta yankewa ma safarar miyagun kwayoyin tarar N250,000.

An dai kama Danladi ne a ranar 20 ga watan Oktoba 2020 kusa da ofishin hukumar NDLEA da ke karamar hkumar Langtang North ta jihar Filato.

“Kotu ta yi masa afuwa ne musamman don ganin lauyansa ya meni masa afuwa a gaban alkalin a madadinsa.

Ya kuma ce, laifin ya saba wa shashi na 19 na dokokin hukumar NDLEA Act CAP 30 na shekarar 2004.

Share.

About Author

Leave A Reply