Kotu Ta Umarci A Kulle Wasu Abokai Biyu Saboda Yi Wa Yarinya Fyade

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A ranar Laraba ne kotun Majastare da ke Ikeja, Legas, ta umarci a gaggauta wucewa da wasu abokai biyu gidan gyara halinka na Kirikiri Legas, saboda yi wa wata yarinya fyade.

‘Yan sanda na tuhumar Tunmise Oladoyin da abokinsa Peter Awe dukkansu masu shekara 24 a duniya da laifin hada baki da kuma yin fyade.

Alkalin kotun, O.A Ajibade, bai tsaya saurarar bayani daga wurin su ba, inda ya umarci a wuce dasu gidan yarin Kirikiri, Lagos ya kuma umarcin a wuce da takardar shari’ar su  zuwa ofishin mai gabatar da kara na jihar don ya bayar da shawarar yadda za a fuskanci shari’a, ya kuma daga kara zuwa ranar 28 ga watan Yuli.

Tun da farko, mai gabatar da karar, DSP Kehinde Ajayi, ya bayyana wa kotun cewa, wadanda ake zargin, Oladoyin da Awe, dukkansu suna zaune ne a unguwar Apapere a yankin Ketu ta jihar Legas sun kuma aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Mayu a otal din Toazan da ke layin Tinubu, Alapere.

Ya kuma kara da cewa, Oladoyin da Awe sun yi ta jima’i ne da yarinyar, daga baya ne iyayen yarinyar sa kai kara ofishin ‘yan sanda da ke Ketu, inda suka gudanar da bincike, anan ne wadda aka yi wa fyade ta tabbatar da gane Oladoyin da Awe a matsayin wadanda suka yi mata fyade. Ya kuma ce laifin sun saba wa sashi na 137 da 411 na dokokin manyan laifukka na jihar Legas.

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply