Kungiyar ActionAid Ta Nemi A Inganta Jindadin ‘Yan Jarida A Nijeriya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kungiyar ActionAid reshen Nijeriya ta bukaci masu gidajen jarida su tabbatar da suna biyan ‘yan jarida cikakken hakkokinsu.

Shugban kungiyar a Nijeriya, Ene Obi ta yi wanna kiran a cikin bukukuwan ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya a tattaunawarsa da manema labarai a garin Kaduna ranar Litinin.

“’Yancin ‘yan jarida na daya daga cikin ginshikin mulkin dimokradiya, ya kuma kamata a sama musu yancin in har ana so su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

“Ya kuma kamata masu gidajen yada labarai su tabatar da biyan ‘yan jarida dukkan hakkokinsu,” inji Obi.

Ta kuma nuna rashin amincewarta akan yadda gwamnati da hukumomin da ba na gwamnati ba ke danne hakkokin ‘yan jarida a yayin da suke gudanar da aikin su a Nijeriya, hakan yana kawo cikas ga aikin da ‘yan jaridar ke yi a kasar nan.

Ta kuma tunatar da cewa, gwamnatin Nijeriya ta yi alkawarin kare hakkin ‘yan jarida tare da basu hakkokin su a shekarar 2018, amma kuma abin takaici shi ne gwamnatocin da suka biyo baya sun kasa cika wanna alkawarin.

Daga nan ta kuma shawarci gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki su kara sakewa yan jarida mara tare da biyan su hakkokin su gaba daya.

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply