Kungiyar Kwadago Ta Gargadi ‘Yan Nijeriya Kan Siyasantar Da Lamarin Tsaro

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kungiyar kwadago reshen jihar Ebonyi ta yi gargadi a kan yadda wasu shugabanin al’umma da ‘yan siyasa ke neman a siyasantar da lamarin matsalar tsaro da ake fuskanta a fadin kasar nan.

Shugaban kungiyar, Mr Ikechukwu Nwafor, ya yi wannan gargadin a tattauwarsa da manema labarai dangane da bukukuwan ranar ma’aikata ta wannan shekarar a garin Abakaliki ranar Asabar.

Ya kuma yaba wa matakan gwamnati daban daban akan yadda suka fuskanci annobar cutar korona da kuma yadda suka dakile bazuwarta a Nijeriya.

Ya kuma yi tir da yadda ake kashe jama’a a fadin kasar nan, kisan da ‘yan ta’adda ke yi ba tare da kakkautawa ba, “Muna kira ga masu aikata wannan aika-aikar su gaggauta tuba tare da barin kisan jama’a.

“Dole gwamnati a dukkan matakai su hada hannu wajen ganin bayan ‘yan ta’adda tare da kuma kare rayuwar al’umma musamman al’ummar jihar Ebonyi.

Akan abubuwan jin dadin ma’aikata, shugaban kungiyar ya bukaci gwamnati ta cika dukkan alkawurran da ta dauka na bunkasa rayuwar ma’aikata a jihar tare da biyan albashi ba tare da bata lokaci ba.

Share.

About Author

Leave A Reply