Kungiyar Kwadago Ta Nemi Ganduje Ya Biya ‘Yan Fansho Bashin Naira Biliyan 26 Da Suke Bin Gwamnati

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kungiyar kwadago reshen jihar Kano ta yi kira ga Gwamnan jihar Abdulahi Ganduje da ya duba bukatar biyan ‘yan fansho bashin fiye da Naira Biliyan 26 da suke bin gwamnati, kudaden ritaya da kuma na wadanda suka rasu a bakin aiki.

Shugaban kungiyar, Mr Kabir Ado-Minjibir, ya bayyana haka a taron manema labarai a ranar Asabar a cigaba da bukukuwan ranar ma’aikata na wannan shekarar ‘2021 workers’ day’.

Shugaban kungiyar ya ce, biyan kudaden na daga cikin bukatun da suka mika wa gwamnatin jihar, sauran kuma sun hada da neman gwamnati ta biya musu bukatan.

Sauran bukatun sun hada da sake duba shekarun yin ritaya na ma’aikatan kananan hukumomi kamar yadda aka sake duba na malamai, daga shekara 35/60 zuwa shekara 40/65.

“Yin haka zai rage yadda masu karbar fansho ke kara karuwa a cikin shekaru biyar da suka wuce, wanda haka kuma yana kara yawan ‘yan fansho a jihar abin da kuma yake kara yawan kudaden fansho da ake biya a jihar.

“Muna kuma bukatar gwamnati ta samar mana da tashoshin mota a tsarin motocin haya da muke shirin samarwa a jihar.

 

Share.

About Author

Leave A Reply