Kungiyar Kwallon Kafa Ta Nasarawa United Ta Amince A Yi Bincike Kan Yadda Dan Wasanta, Martins Ya Mutu

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugabannin Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United sun amince a yi bincike don gano musababbin rasuwar dan kwallonta, marigayi Chineme Martins.

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da jami’in watsa labaran kungiyar, Eche Amos, ya bai wa Kamfanin dillancin labaran Nijeriya, NAN, a Lafiya ranar Talata.

A cewar Eche, an dauki wannan matakin ne bayan tattauna tsakanin shugabannin kungiyar da makusantan mamacin ranar Litinin a garin Lafiya.

“A cikin zama akwai ‘yan uwan marigayi Martins na jini, wanda yayanshi, Michael Chineme, ya jagoranta, da kuma shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United karkashin jagorancin Isaac Danladi.

“Matsayar da aka cimma tsakanin bangarori biyun shi ne, a yi bincike don gano asalin dalilin mutuwarsa,” inji Amos.

Eche ya kuma yi alkawarin kungiyar za ta karrama dan wasan nata da gagarumar jana’iza.

Idan ba a manta ba, marigayi Martins ya yanki jiki ne yayin da suke kan fafatawa da kungiyar kwallon kafa ta Katsina United ranar Lahadin da ta gabata a filin kwallon kafa na garin Lafiya.

An yi  kokarin ya farfado amma bayan an kai shi Asibitin kwararru na Dalhatu Araf sai aka gano ya riga mu gidan gaskiya.

 

Share.

About Author

Leave A Reply