Kungiyoyin Kwadago Sun Yi Zanga-zanga A Jami’ar Jihar Legas Kan Mafi Karancin Albashi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kungiyoyin kwadago na cikin Jami’ar Jihar Legas, LASU, da ke Ojo ranar Litinin sun tare hanyoyin shiga makarantar, matakin da ya hana malamai da dalibai hanyar shiga makarantar.

 

Rahotanni sun tabbatar da cewa wakilan kungiyoyin sun na zanga-zangar rashin fara biyan su mafi karancin albashin ne gwamnatin jihar Legas ba ta fara yi ba.

 

Kungiyoyin sun hada da: Kungiyar malaman jami’a ta ASUU, Kungiyar ma’aikatan jami’a ta NASU da kungiyar manyan ma’aikatan da ke aiki a jami’o’i ta SSANU.

 

Kungiyoyin sun bukaci hukumomin gudanar da Jami’ar ta LASU da su koma aiki a Ma’aikatar ilimi da ke Alausa a Legas.

 

 

Rahotanni na nuna cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi umurin manyan makarantun jihar su bude ranar 14 ga watan Satumba.

 

 

 

Sannan a ranar 18 ga watan Afrilun shekarar 2019, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a fara biyan ma’aikatan kasar mafi karancin albashin naira 30,000.

Shugaban ASUU, reshen Jami’ar LASU, Dakta Ibrahim Bakare, ya ce ba za a bude jami’ar ba, matukar ba a biya mambobinta mafi karancin albashin ba.

 

 

Bakare ya ce ma’aikatan dukkan makarantun jihar Legas sun cimma matsayar kin bude makarantu, idan gwamnatin jihar ba ta fara biyansu mafai karancin albashi ba.

 

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply