Kyawun Alkawari Cikawa: Mai’adua Muna Sauraron Gwamna

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Umar Sani Lalu
Alkawali yana daya daga cikin abubuwa masu girma da muhimmanci a rayuwar mu ta musulmai. AlQur’ani da Hadisan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sunyi nuni akan haka a wurare da dama da kuma illar kin cika alkawali.
Sai dai a yanzu karya alkawali da kin cika shi a tsakanin mutanen mu ya zama ruwan dare. Bugu da kari kuma sai gashi yanzu rashin cika alkawali ya zama wata al’ada musamman shugabanni.
Idan lokacin zabe ya taho ana yakin neman zabe zaka ga yantakara na mukamai a matakai daban daban sunayiwa masu zabe alkawulla iri iri domin su kada masu kuri’a lokacin zabe.
Amma da zaran an ci zabe za muga irin wayannan alkawullan an rufe shafin su ta yadda bama sa so suji alkawalin da sukayi ballantana ma su dauki matakan cikawa har sai wani zaben ya dawo kaga ana bada hakuri har da neman yafiya akan rashin cika alkawullan baya da shan alwashin cikawa.
Sau tari akan yiwa masu zabe romon baka da wani abuda yafi damun su domin karfafa masu gwiwwa su marawa Dan-Takara da jam’iyyar sa baya.
Irin wannan alkawalin ne a kayiwa mutanen mu Karamar Hukumar Maiadua a lokacin yakin neman zaben shekara ta 2015 da Mai-Girma Gwamnan Katsina yayi zai daga darajar karamin asibitin Maiadua zuwa babban asibitin kwanciya (General Hospital).
Jin wannan alkawali yayiwa mutanen Karamar Hukumar Maiadua dadi ganin wannan yana daga cikin manyan matsalolin dake damun mutanen Maiadua domin idan marassa lafiya suka zama suna bukatar kulawa ta musamman sai sun tafi Daura koma sai an dangana da Katsina.
Yin wannan aiki zai kawowa mutanen kauyuka da masu karamin karfi saukin matsalolin kula da lafiya.
Sai dai tafiya ta mika, an gama zangon farko na mulkin Mai-Girma Gwamna 2015-2019 wannan alkawali ba’a cikawa mutanen Karamar Hukumar Maiadua shi ba kuma gashi Zango na biyu har ya raba bamu ga alamu ba na Gwamnati da gaske take wajen daga darajar karamin asibitin Maiadua zuwa babban asibitin kwanciya ba.
Karamar Hukumar Maiadua tana daya daga cikin kananan hukumomi dake Jahar Katsina wayanda ke kan gaba wajen samun kudaden shiga wanda idan aka ririta su za’a iya yiwa mutanen Maiadua wannan aiki ba tare da an dauki wani dogon lokaci ba.
Amma sai gashi kusan wankin hula na neman yakai Gwamnatin Katsina dare ga kuma zabe na 2023 na karatowa. Ko babu kome muna bibiyar alkawullan da, akayi mana a baki da har yanzu bamu gani a kasa ba.
Babu ko shakka, alkawullan da aka cikawa jama’a suna tasiri wajen kara marawa gwamnati mai ci baya ko akasin hakan lokacin zabe.
Sai dai kuma wani hamzari ba gudu ba idan a kayiwa gwamnati tuni akan alkawalin da ta dauka sai kaga anyiwa mutum mummunar fassara kawai saboda, yayiwa gwamnati matashiya na cika, alkawali.
Jama’a, sai muyi karatun ta, nutsu muga wane abubuwa akayi mana alkawali aka cika ko akasin hakan.

Umar Sani Lalu
Maiadua

Share.

About Author

Leave A Reply