La Liga: Levante Ta Tozarta Real Madrid

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A daren jiya ne kungiyar kwallon kafa ta Levante ta yi wa babbar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ci daya mai ban haushi.

Wannan nasara ta Levante a kan Real Madrid ne ya sa ta yi watsi da damar da kungiyar ke da ita akan Barcelona na kasancewa ta daya a saman teburin La Liga

Kungiyar Barcelona wacce za ta buga wasa da Real Madrid a ranar Lahadi mai zuwa, ta samu karin maki biyu bayan ta yi wa kungiyar Eibar 5-0.

Ana iya cewa Kungiyar Real Madrid ba ta yi wani kokari ba a wasan nata da Levante, domin kuwa da Levante ta zura kwallayen da ta kai farmaki, da sakamakon wasan ya wuce haka.

Share.

About Author

Leave A Reply