Ma’aikatan Jami’ar Jam’iar ABU Sun Yi Zanga-zangar Rashin Biyan Su Alawus Da Neman Fita Daga Tsarin IPPS

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kungiyar ma’aikatan jami’o’i, NASU, reshen jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta bi sahun takwarorinta na.sauran jami’o’i wajen gudanar da zanga-zangar gargadi ga gwamnatin tarayya.

Da sanyin safiyar ranar Laraba, 13/1/2021, mambobin kungiyar suka yi dandazo a harabar jami’ar tare da rera wakokin neman ‘yanci.

Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka shaida yadda al’amarin ya gudana. Kungiyar ta bayyana wasu koke-koke da korafe-korafe da gwamnati ya kamata ta sauraresu amma abin ya ci tura, bisa haka ne wakilinmu ya nemi jin ta bakin sakataren kungiyar kwamret Emmanuel Adugwu dangane da lamari bisa haka ne take sakataren ya shelanta abin dake damunsu kamar haka. Yace ‘Dalilin yin wannan zanga-zangar tamu shine muna neman hakkokinmu ne daga gwamnatin tarayya, tun watan Oktoba akwai maganar alawus dinmu, akwai ariyas na mafi karancin albashi, akwai rashin bin tsari wajen biya da IPPS, akwai kin yin yarjejeniya tsakanin kungiyar mu wanda gwamnatin tarayya ta yi da kuma rashin biyan mambobinmu da suka bar aiki. Shi ya sa muka fito domin nunawa gwamnatin tarayya cewa ba ta dube mu ba, ba ta yi gyara ga al’amurran da muka bayyana ba.’

Ya ce ya kamata gwamnati ta lura da halin matsi da ake ciki, kamar hauhawar farashin kayan abinci da na kayan masarufi da ya shafi lafiya da harkokin sufuri, ya ce bisa hakane kungiyar ta fito kwanta-da-kwarkwata ta yi zanga-zangar gargadi na kwana uku kamar yadda doka ta tanada kuma ya yi kira ga ‘ya’yan kungiyar da su bada hadin kai ga kungiyar baki daya. Ya ce hakan ne zai haifar da nasara. Kuma ya yi kira ga gwamnati da ta kasance mai cika alkawurranta, domin hakan ne zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

An yi taro lafiya an tashi lafiya

Share.

About Author

Leave A Reply