Ma’ikaciyar Banki Ta Saci Naira Miliyan 2 Daga Asusun Ajiyar Abokin Huldarsu

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

An gurfanar da wata ma’aikaciyar Banki mai suna Jessica Ogba, mai shekatra 32 a duniya a gaban kotun majastare da ke unguwar Tinubi Legas akan sace Naira Miliyan daga asusun abokin huldarsu.

Sai dai Ogba, ta musanta aikata laifin a yayin da aka karanto mata tuhumar da ake yi mata a gaban kotun.

Mai gabatar da karar, ASP Ben Ekundayo, ya bayyana wa kotun cewa, wanda ake tuhumar ta aikata laifin ne a ranar 25 ga watan Janairu da misalin karfe 11:00 a Murtala Muhammad Way, Ebute-Metta, Legas.

Ya ce, wanda ke zargin na aiki ne tare da daya daga cikin tsofaffin banbkuna kasar nan inda ta samu sa’ar sace Naira Miliyan 2 daga asusun wani mai jiya a Bankin.

Ya kuma ce, laifin ya saba wa shashi na 287 (7) na dokokin manyan laifukka na jihar Legas na shekarar 2015.

Alkalin kotun, Mr A.A. Paul ya bayar da belin wadda aka zargin akan kudi Naira 200,000 ya kuma daga karar zuwa ranar 5 ga watan Afrilu.

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply