Martani: Matsalolin Rashawa Sun Jefa Fadar Shugaban Kasa A Tsaka Mai Wuya, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Marigayi Mahatma Ghandi ya taba cewa kafafen watsa labarai manyan turaku ne wurin kawo sauyi. Sai dai ya yi gargadin cewa idan aka tafiyar da kafafen ba ta hanyar da ta dace ba, maimakon su kawo sauyi na ci gaba, sai su haifar da Baraka. Don haka kafafen watsa labarai kamar takobi ne mai kaifi biyu, za a iya aikata barna da shi, ko a aikata alheri.

Na yarda da matsayar Chinua Achebe da yake cewa, “Lokacin da abubuwa ba su tafiya yadda ya dace, hakki ne da ya rataya akan marubuci ya bayyana su.” Amma wannan sam ba dalili ba ne da zai sa wani ya rika yada labaran bogi, karya ko sharri domin son ranshi.

Irin wannan mugun yanayin jaridar Desert Herald ta ke kokarin jefa aikin jarida, duk bisa son ransu na haifar da rikici. A wani rahoton jaridar wanda ta yi wa take da “Yawaitar Matsalolin Rashawa Sun Jefa Fadar Shugaban Kasa A Tsaka Mai Wuya’. Marubucin ya yi ta kokarin sai ya nuna cewa gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cike take da cin hanci da rashawa. Wuce nan, ya karkare da cewa rashawa ce dabaibaye da gwamnatin.

Kun ji wata shirgegiyar karya! A tarihin Nijeriya babu wani Shugaba da gwamnatinsa ta ke tsarkake hatta mutanen cikinta daga harkar rashawa sai gwamnatin Buhari, wanda hakan ya kamata duk wata gwamnatin kwarai ta aikata.  Ko ta ya wadannan masu son haifar da rikicin suke so shugaba Buhari ya nunawa duniya cewa shi makiyin cin hanci ne? Ko ba komi Jaridar Desert Herald ta san cewa, Buhari bai zo don yin wasa da cin hanci ba.

Babu bukatar sai an tsaya ana tunatar da wadannan mashirmatan yadda gwamnatin Shugaba Buhari ta dawowa da Nijeriya Dala Biliyan Biyu na kudin makamai. Da gangan gwamnatin Buhari ta ki fallasa matakan bincike da tsarin binciken kudaden makamai, saboda kar hakan ya haifarwa da binciken cikas. A lokacin da aka kammala binciken za a sha mamaki, domin mutane da yawa za su tafi gidan yari.

Babu tantama, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana iya kokarinsa wurin ganin ya tsarkake Nijeriya daga muguwar dabi’ar cin hanci da rashawa. Duk da an daure da yawa, amma duk wanda ke da hannu a badakalar kudaden makamai ba zai sha ba, don su ne suka jefa ‘yan Nijeriya cikin halin rashin tabbas daga rashin tsaro.

A gwamnatocin baya, Hukumar Kula da Ci gaban Neja Delta (NDDC) ta kasashen tamkar wata saniyar tatsa a wurin manyan mutane daga yankin. Sai bayan da gwamnatin Shugaba Buhari ta zo sannan aka fara sanin hakikanin irin badakalar da ake aikatawa a NDDC. A matsayinsa na shugaban da bai tsayawa wata-wata ko muna-muna, Shugaba Buhari ya bayar da umurnin a gaggauta binciken zargin badakala a hukumar. Kuma zargin wai gwamnati na kokarin bayar da kariya ga Madam Joy Nunieh ne wannan ba karamar rainin hankali da wasa da hankali ba ne.

Yana da kyau mu sanar da wadannan makiya na Nijeriya cewa, gwamnatin Shugaba Buhari ta gwada gaskiya a yanayin gudanar da gwamnati a bayyane ba tare da wani boye-boye ko munafurci ba. Ai duk muna gani yadda gwamnati ta saki Kanar Dasuki duk da tarin zargin cin hanci da rashawar da ke kansa. A yanzu a Nijeriya babu wani wanda ake daure da shi da sunan siyasa. Wannan kadai ya nuna biyayyar Buhari ga dokokin kasa.

Kuma ya zuwa yanzu Buhari ya nuna cewa shi Uba ne wanda hatta ‘ya’yansa ba ya zuba musu ido su yi ba daidai ba. Kowa ya san yadda muka yi ta caccakar majalisa ta takwas saboda kin tabbatar da Magu a matsayin Shugaban EFCC. Amma da shugaban Kasa ya samu dalilan bincikar Magu, bai yi kasa a gwiwa ba, saboda ba ya kaunar cin hanci da rashawa. Ina ga ai kamata ya yi Jaridar Desert Herald ta yabawa Shugaban a bisa wannan ba wai su hau ci mashi mutunci ba.

A bayyane yake cewa Desert Herald ta kirkiri wannan hayaniyar ne da niyyar batanci da cin mutunci. Sun rufe idonsu daga ganin yadda aka cafke Okoi Obono-Obla bisa zargin cin hanci da rashawa. Wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa na musamman mai binciken lamurran cin hanci da rashawa.

A burinsu na son bakanta sunan Kare domin su rataye shi ne ya sa ba su ganin alherai da kokarin wannan gwamnatin a fagen yaki da cin hanci da rashawa.

Jaridar bata tsaya a nan ba ta ci gaba da zargin cewa kaf cikin gwamnatin nan babu wani mutum daya da ke iya shiga ya yi sulhu a tsakanin ma’aikatan gwamnati yayin da abubuwa suka rincabe. Wannan zargin ya kara nuna burinsu na son ganin sun haifar da sabani da rikici. Idan bah aka ba, me ya sa suke ta kurari da biyewa makiyan Nijeriya wurin jifan gwamnati da maganganun banza da kazafi da sharri?

Idan ba a manta ba, Kungiyar Kasashen Afirka bayan da ta fahimci irin rawar da shugaba Buhari ke takawa a kan harkar cin hanci, ta ba shi kambun sarkin yaki da rashawa na Afirka. Toh sai kuma me wadannan makaryatan suke nema?

Aikin jarida aiki ne na samar da ci gaba, ba aikin son rusa wani ba. Jaridar Desert Herald da masu daukar nauyinsu ya kamata su san cewa zamanin yin amfani da karairayi domin tunzura ‘yan Nijeriya kan shugabanninsu ya wuce. ‘Yan Nijeriya sun kara wayewa, kuma a shirye suke su ba shugaba Buhari gudummawa domin tabbatar da nasara a ajandarsa ta mataki nag aba.

– Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da Tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa ‘Presidential Support Committee’ (PSC)

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply