Matsalar Tsaro: Gwamnati Na Shirin Yi Wa Dokar Zirga-zirga Na ECOWAS Kwaskwarima

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnain tarayya ta ce, a halin yanzu tana kokarin ganin a yi wa dokar zirga-zirga na al’umma da dabbobi a tsakanin kasashen yankin Afrika ta yamma ECOWAS kwaskwarima don kawo karshen harkokin yan ta’adda.

Minitan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana haka a ranar Asabar a shirin gidan talabijin na Channels mai suna “Sunrise Daily’.

Ya ce, yawanci ‘yan ta’addan makiyaya da ke addabar yankunan Nijeriya ba ‘yan Nijeriya bane.

Ya ce suna shigowa kasar ne ta iyakokin kasa saboda dokar ECOWAS da a amince da zirga-zirgar al’umma a tsakanin kasashe ba tare da wani matsala ko takurawa ba.

“Dokar ECOWAS ta yarje da a bar al’ummar yankin su yi zirga-zirga ba tare da wani mastala ba a tsakanin kasashen yankin.

“Akan haka muke shirin ganin mun nemi a yi wa dokar kwaskwarima don kare yan ta’adda shigowa kasar nan.

Ya kuma ce manyan matsalolin tsaro da ke fuskanta sun hada da na makiyaya na manoma da kuma na sace sacen jama’a wanda kuma ba a lokacin wannan gwamnatin aka fara ba.

Share.

About Author

Leave A Reply