Matsalolin Tsaro Sun Dusashe Hasken Bikin Ranar Dimokradiyya Ta Bana

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Ado Umar Lalu

Mulkin dimokaradiyya yana bai wa yankasa dama da yancin fada aji wajen tafiyar da gwamnati ta hanyar zaben shugabanni da zasu ja ragamar al’amuran su a matakan gwamnati daban daban.
A duk lokacin da talakawa suka zabi gwamnatin da suke so yana saka masu kyakkyawan fata a ran su na samun sauki da ingantuwar rayuwar su, a dukkan fannonin rayuwa.
Irin wannan damar da salon mulkin dimokaradiyya tasa ake ware wata rana domin ayi waiwaye wanda hausawa ke cewa adon tafiya domin ganin irin matsalolin da cikas da aka fuskanta da kuma nasarorin da aka samu wajen cigaban kasa da al’umma baki daya domin ayi gyara ta yadda za’a kara inganta rayuwar jama’a da habaka tattalin arziki.
Sai dai zamu ce a wannan biki na bana wanda shine na farko da aka gudanar da shi a ranar 12 ga watan Yuni saboda tunawa da zaben 12 ga watan Yuni na 1992 da Dankarar Jam’iyyar SDP Chief MKO Abiola ya kama hanyar lashewa da gagarumin rinjaye kafin Shugaban Mulkin Soja na lokacin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya soke baiyi ar’mashi ba saboda dinbim matsalolin da sukayiwa kasar katutu musamman a arewacin kasar.
Hakika mutanen arewacin Nigeria sun bada gagarumar gudunmawa da taka rawar azo agani wajen cin zaben Shugaba Muhammadu Buhari inda a karon farko jam’iyyar adawa ta kayar da jam’iyya mai mulki.
Mutanen arewa sun nunawa jam”iyyar APC kauna irin wadda basu nunawa wata jam’iyya a kasar na saboda yarda da kuma ammana da sukayi da jagoran ta na samun kyautatuwa da samun ingancin rayuwa musamman tabarbarewar tsaro wadda ta jefa rayuka da dukiyoyin yan-arewa cikin hadari sakamakon hare haren boko-haram, masu satar shanu, yanfashi da makami da kuma garkuwa da jama’a domin karbar kudin fansa.
Hakika zuwan gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taka gagarumar rawa wajen dakile hare haren yanboko-haram da yakai ga kwato dukkan kananan hukumomin da suka kwace da samun raguwar ko kawo karshen tashe tashen bamabamai a arewacin kasar. Sai dai kawo yanzu a tsawon shekaru biyar na mulkin APC kamar yadda tayi alkawali da shan alwashin kawo karshen ayyukan tarzoma na boko-haram da kakkabe su abun dai za’ace wankin hula ya kai ta dare domin ko a wannan mako mai karewa sai da yanboko-haram suka kai mummunan hari a garin Gubuyo na Jahar Borno inda yayi sanadiyyar rasa rayukan sama da mutane sitti tare da kone masu gidaje da kayayyakin su. Wannan ya nuna akwai sauran rina a kaba da kuma jan aiki a gaban wannan gwamnati gashi kuma lokaci na neman kurewa.
Baya ga matsalolin boko-haram hare haren barayin daji masu garkuwa da mutane, kisan gilla, sace kaya dayiwa mata fyade sun zama ruwan dare a arewa maso yamma. Wayannan matsaloli suna ci gaba da barazana da kawo cikas ga rayuwa da dukiyoyin yan-arewacin Nigeria.
Sakamakon ayyukan yantaadda duk masu safara akan hanyar Kaduna zuwa Abuja kullum suna cikin zullumi saboda yadda ake farautar mutane. Irin wayannan matsaloli sun sa bin hanyar Kaduna zuwa Birnin-Gwari da kuma Birnin-Gwari zuwa Funtua sun zama masu hadari ga masu bin hanyar. Jahohin Katsina, Zamfara da kuma Sokoto sun zama wuraren da masu ina da kisa suke cin karen su babu babbaka.
Tabarbarewar tsaro ta sanya mutane a wasu yankunan Jahar Katsina, Sokoto da Zamfara cikin zaman dardar domin tsoron maharan dake afkamasu a duk lokacin da suka ga dama wanda a kwanan sai da ya rutsa da hakimin Yantumaki. Wannan tasanya mutane da dama gudun hijira domin tsira da rayukan su da dan abunda yayi masu saura. Ta kai ga a yanzu mutane a garuruwan da suke fama da irin wayannan matsaloli sun manta da maganar sama masu kayan more rayuwa sun mayar da hankalin su akan sama masu tsaro wanda suke ganin gwamnati ta gaza duk shirin da gwamnati ta bullo dashi na OPERATIONS HARBIN KUNAMA a farkon hawanta domin kakkabe barayin shanu amma kawo yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba ballantana ayi maganar riba.
Mutanen wannan yanki da kusan sune suke noma abincin da ake kaiwa sansan jahar da makwabtan jahohi har zuwa Jamhuriyyar Niger, sakamakon ayyukan maharan daji sun kawo raguwar noma a yankin wanda matsalolin tsaro suka haddasa. Idan har gwamnati bata dauki matakin gaggawa ba na magance matsalolin tsaro a arewacin Nigeria ba to babu ko shakka zai haifar da karancin cimaka da zai sanya abinci yayi tsada kuma ya haifar da talauci a tsakanin manoma da makiyaya.
Tun kafin matsalolin tsaro su kara ta’azzara ansha yin kiraye kiraye ga Shugaban Kasa da ya kawo sauye sauye a gwamnatin sa domin shawokan wannan barazanar tsaro ta hanyar tankade da rauraya a rundinonin tsaro na kasar na musamman manyan kwamandoji da ake ganin lokacin su ya wuce amma an kara masu waadi wanda tabbas zai sanyan na kasa suyi zamam dirshan tunda babu matsawa zuwa mukami na gaba.
Ina roko da kuma kira ga shugabanni da nauyin kare rayuka da dukiyoyin jama’a ke kansu da su rinka sauraron koke koken jama’a domin a kawo gyara da sauyi inda ya kamata a gyara ba tare da bata lokaci.
Har ila yau ya kamata Shugaban Kasa ya kafa wasu kwamitoci na kwararru da zasu duba alkawullan da yayiwa mutane domin ganin shin an aiwatar dasu a aikace ko kuma har yanzu suna kan takarda ne, in an fara to ina aka tsaya kuma yaya za’a kai ga kammalawa.
Bugu da kari mutanen arewa da suka bada gagarumar gudunmawa dayiwa APC ruwan kuri’u wanda ya bata nasarori a zabukan baya suna ganin wannan gwamnati ta zama ta yarabawa inda sune suka kankane mukaman gwamnati da kuma ayyukan raya kasa kamar su layin dogo, tituna da dai sauran su domin ganin idan zabukkan 2023 suka zo APC zata nunawa yan-arewa ayyukan da akayi masu a zahiri domin kara samun lamuncewar na sake kada mata kuri’u kafin lokaci ya kure.
A daidai lokacin da nake wannan sharhin saii ga labarin kisan Mai-Garin Mazoji dake Karamar Hukumar Matazu a yau dinnann 13 ga watan Yuni na wannan shekara. Baba Buhari muna kaunar kuma muna son ganin yankunan mu sun zauna lafiya. Abunda yaci Doma ba zaibar Awe, matsalolin tsaro su suka durkusar da PDP kuma gasu sunyiwa APC lale maraba sun kunno wuta a Jahar ka.
Ado Umar Lalu
adoumarlalu57@gmail.com
+2348060306089

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply